Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar da fom domin sake tattara sakamakon zaɓen gwamna na wasu yankuna a ƙaramar hukumar Fufore ta Jihar Adamawa.
Hakan na zuwa ne bayan rikicin da ya ɓarke a ƙaramar hukumar inda ’yan bata-gari suka yi ɓarna.
Kwamishinan zaɓe na jihar (REC), Hudu Yunusa-Ari, da yake gabatar da tambayoyi daga manema labarai a ranar Lahadi, ya ce hukumar ba ta da wani ɗan takara kamar yadda ya ce ana zarginta da shi.
Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa za a bayyana wanda ya lashe zaɓen kamar yadda dokar zaɓe ta tanada.
Wakilin tattara sakamakon zaɓe na jam’iyyar PDP a jihar, tsohon ƙaramin ministan lafiya Dakta Idi Hong ya koka da yadda aka kwace takardar sakamako a ƙaramar hukumar Fufore.
A lokacin gabatar da wannan rahoto, Gwamna Umaru Fintiri na jam’iyyar PDP yana kan gaba da ƙananan hukumomi 11 daga cikin 18 da INEC ta sanar.
Ana ci gaba da sa ran samun sakamakon ƙananan hukumomi uku, wato ƙaramar hukumar Song, Michika da Fufore.