INEC za ta yi kaka-gida a rumfunan zaɓe don hana sayen ƙuri’u

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gabanin zaɓen shekarar 2023, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce, za ta magance matsalolin da suka sava wa doka kan kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe da kuma abin da ta kira ‘al’adar sayen kuri’u’ a rumfunan zaɓe a ranar zaɓe’.

Don haka, hukumar ta ce, a jiya Alhamis, 24 ga Nuwamba, 2022 ne ta fitar da taƙaitaccen bayani kan ƙa’idojin kuɗi da kuɗaɗen zaven jam’iyyu da ’yan takara.

Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana haka a ranar Laraba a wani taron masu ruwa da tsaki da ƙungiyar ‘Civil Society Situation Room’ (CSSR) ta shirya a Abuja.

Ya ce, “idan muka koma kan kuɗin yaƙin neman zaɓe, hukumar ta ƙudiri aniyar tunkarar lamarin tun da farko. Abubuwan karya dokar sun haɗa da kashe kuɗaɗen jam’iyya da ’yan takara fiye da yadda doka ta tanada da kuma tsarin sayen ƙuri’u a rumfunan zaɓe a ranar zaɓe.

“A nan kuma, a ranar Alhamis 24 ga Nuwamba, 2022, hukumar za ta fitar da takaitaccen bayani kan ƙa’idojin kashe kuɗi da kuɗaɗen zaɓen jam’iyyu da ’yan takara.

“Bayan haka, muna ƙara haɗa kan kowace cibiya ta ƙasa da alhakin bin diddigin yadda ake tafiyar da kuɗaɗe da kuma hukumomin yaɗa labarai da na buga jaridu don tunkarar matsalar gaba ɗaya. Za a bayyana cikakken bayanin hakan nan ba da jimawa ba.”

Har ila yau, hukumar ta bayyana cewa ta sake ganawa da shugabannin ƙungiyar ma’aikatan tituna ta ƙasa tare da sake duba yarjejeniyar fahimtar juna da ƙungiyoyin da ke kula da tituna.

A yayin da ta ke bayyana cewa an samu gagarumin cigaba wajen samarwa da kuma kai muhimman kayan zaɓe ga ofisoshin INEC na jihohi da kuma cigaba da ɗaukar sabbin ma’aikata da horar da ma’aikatan wucin gadi, hukumar ta ce, ta faɗaɗa aikin haɗin gwiwa zuwa ga ma’aikatun zaɓe da ƙungiyar yankuna.

Da ta ke magana kan fasaha, hukumar ta ce “dokar zaɓe ta 2022 ta buƙaci hukumar da ta tura fasahar na’ura ranar zaɓe domin tantance masu kaɗa ƙuri’a da kuma shigar da sakamakon zaɓen zuwa tashar INEC Result Viewing (IReV). Za a cimma waɗannan matakai ta hanyar amfani da Tsarin Tabbatar da Zaɓe na Bimodal (BVAS).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *