Daga BASHIR ISAH
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya sake lashe zaɓe a matsayin Gwamnan Jihar Gombe ƙarƙashin Jam’iyyar APC a zaɓen gwamnoni na 2023.
Ya lashe zaɓen ne bayan da ya samu mafi yawan ƙiri’u a ƙananan hukumomi 11 da jihar ke da su.
A ranar Lahadi Baturiyar zaɓe a jihar, Farfesa Maimuna Waziri ta ayyana Inuwa a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri’u 342, 821.
Wannan shi ne karo na biyu da Inuwa ke zama gwamna a jihar ta Gombe.