Inuwa zafi, rana ƙuna

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

A lokacin da a ke tsananin zafi mutane kan nemi ruwa mai sanyi ko wajen mai inuwa don rage kaifin ƙalubalen yanayin. A wasu shekaru ma da idan wasu bai gama wayewa ba su kan ɗora ƙanƙara a kansu su kifa hula har ta kai ga an samu matsalar daskarewar jini da kan iya haifar da asarar rai.

Abun da na ke son magana a kai wannan makon shi ne yadda tsananin zafin rana kan ƙare a kan talakawa wajen neman abinci amma ba lallai ne su samu ba don yadda rayuwa a zamanin yau ta zama da ɗan karen tsada.

A gefe guda don maganin zafin rana wasu kan fake a inuwa amma ba sa samun sararawar da su ke buƙata don wa imma ba iska da ke kaɗawa a gari ko kuma iskar zafi ta ke turowa saboda tsananin shigowar hamada daga arewaci zuwa kudancin yankunan Sahel ko Sahara. In zafi ya ishi mutum a ɗaki zai so fitowa waje don shan iska tun da ba wadatar lantarki da talakawa za su iya kunna na’ura.

Ai ko da lantarkin ba dukkan talakawa ke iya mallakar fanka ba. In mutum ya fito waje da dare ya kan iya rashin sa’a barawo ya lallaɓo ya yashe ma sa kaya ko kuma in varawo bai shigo ba a samu tarin sauro su addabi kunnuwan talaka su iya zuba ma sa cutar zazzaɓi.

Cikin rahamar ubangiji maɗaukakin Sarki duk lokacin da asuba ta kawo kai a kan samu saukin tsananin zafi. Duk ma a nan mu na magana ne kan sauyin yanayi kafin ya zama shimfiɗar sauyin aljihu ko rashin ƙarfanfana. Da alamu zai yi wuya a lokaci ɗaya a iya yaƙi da gaiyato hamada da mutane musamman mazauna arewacin Nijeriya ke yi saboda dalilai na tattalin arziki.

Sare bishiyoyi don iccen girki ko kona itatuwa don samar da gawayi ya zama ruwan dare. Tun mutane ba sa gane illar yin hakan har yau sun gane don yadda ƙura kan taso ta bule su ko ma ta shiga idanun su. In ka na tafiya a garuruwan arewacin Nijeriya za ka riƙa cin karo da motoci ɗauke da itatuwa ko gawayi don yin girki. Har a wannan sabon zamani akasarin gidajen talakawa kan dogara kan ita ce ko gawayi wajen samun makamashi don shi ne za su iya cijewa su saya.

Rashin wadatar da wasu hanyoyin samar da makamashi da talakawa za su iya mallaka ya sa yaki da sare bishiyoyi ke da wuya. Duk da haka ya zama mai muhimmanci a wayar da kan masu sare itace su riƙa dasa wani a gurbin sa don amfanin gobe. Rahamar Allah kan dawo da wasu bishiyoyin a lokacin damuna ba wani ƙoƙarin masu wargaza dazuka ba.

Abu biyu ke kan gwamnati shi ne ta tilasta dasa bishiyoyi da shiga cikin dashen da kan ta sai kuma ɓullo da dabaru masu araha da za su iya maye gurbin itace. Hakika akwai fasahar da za a iya ƙarfafawa da za ta sa talakawa barin itace don samun makamashi da ma ba ya gurbata yanayi. Samar da makamashi daga hasken rana ko ma daga ruwa abu ne mai yiwuwa daga gwamnati.

Ma’aikatun kimiyya da fasaha su maida hankali wannan ɓangare don ɗora mutane kan hanya mai sauqi da kare lafiyar muhalli. Kowace anguwa kan iya mallakar ofishin bun koasa wannan fasaha inda mutane za su riƙa tuntuɓa don samun wayewa kan hanyoyin binciken kimiyya da kan sauƙaƙa rayuwar jama’a.

In mutane su ka bi sahun kimiyya za su gane ashe kaza ce ta shafe zamani ta na kwana kan dami cikin yunwa. Tsarin zai samar da ayyukan yi. Ina ganin makeran gargajiya da ke garuruwan su za su iya zama hanyar bunƙasa fasahar samar da makamashin da jagoranci daga sassan kimiyya da fasaha na jami’o’i da sauran manyan makarantu.

Kamar yadda Nijeriya ke da tsararrun dokoki da ba duka a ke aiki da su ba to haka a ke da fasahar sauqaqa rayuwa da ba a amfana da ita. Za ka iya samun mutumin da ko kwan lantarki ne ya mutu a gidan sa ba zai iya sauya sabo ba sai ya kira mai aikin wuta ko aninin rigar mutum ya tsinke amma ba zai iya ɗaukar zare da allura ya mayar ba.

Ina mai tabbatar mu ku iya zura zare a hujin allura ma hikima ce ko fasaha ce da ta dace kowa ya iya. Zama ba kataɓus sai dogara kan ‘yan kuɗin da a ka samu wajen samun hidimar rayuwa ta yau da kullum abun takaici ne. Na tava jin wani shugaban Nijeriya na cewa ko tsinken sakace haƙori ba a iya kerawa a Nijeriya sai kenan an shigo da shi daga ƙetare. Kudu ba fa za mu iya faskara katon kututture don iccen dafa abinci amma ba za mu iya sara ko sarrafa itacen wajen samar da tsinken sakace haƙori ba.

Za mu shiga babin halin tattalin arziki da ƙuncin rayuwa da jama’a ke ciki da zummar samo bakin zaren samun sauƙi.

Gwamnan babban bankin Nijeriya Olayemi Cardoso ya ce akwai dalilai waje da batun canjin kuɗi da ke tada farashin kayan masarufi.

Cardoso na magana ne bayan taron kwamitin tsari kan kuɗi na bankin.

Olayemi Cardoso ya ce akwai tashin kayan makamashi da tashin farashin kayan abinci da ke ta’azzara lamuran tsadan.

Kazalika Cardoso ya ƙara da cewa akwai sayan kaya masu ɗimbin yawa da gwamnati ke yi da hakan ke tada farashin kayan masarufi.

Gwamnan bankin ya ba da shawarar duk masu hannu a lamuran tattalin arziki su dau matakan gyara kan damuwar da a ke fuskanta.

Cardoso ya ce su ne dalilan da su ke sa a ke ganin kayan masarufi na ƙara tsada yayin da a ke ɗaukar matakan daidaita darajar Naira.

Kwamitocin Majalisar Wakilai kan man fetur sun bukaci jami’an tsaro su dau matakan daqile masu ɓoye mai.

Shugaban kwamitin raba fetur a cikin kasa Ikenga Ugochinyere ya ce masu ruwa da tsaki na man fetur ciki da kamfanin fetur na NNPCL sun yi mu su bayanin halin da a ke ciki.

Ugochinyere ya ce sun fahimci lamuran sufuri su ka kawo cikas a samar da man in da wasu ‘yan kasuwa ke amfani da damar wajen azurta kan su da ƙazamar riba.

Kwanitocin sun buƙaci jami’an tsaro su taimaka wajen tabbatar da wadatar man ta hanyar hana masu ɓoye man cigaba da karkatar da shi.

Wani abu a fili kuma shi ne taɓarɓarewar tsaro da kan gurgunta kasuwanci, noma da sauran harkokin raya arziki. Kullum labarun tavarvarewar tsaro a ke samu da kan yi sanadiyyar asarar rayuka.

Ɓarayin daji sun auka garin Zurmi a jihar Zamfara inda su ka yi kisan gilla ga mutum 3.

Miyagun sun hari fadar Sarkin Zurmi Muhammad Sulaiman da zummar sace shi amma ba su samu galabar hakan ba.

Baya ga kashe mutum 3 sun sace wasu mutane ciki har da Shamakin Zurmi.

Ɓarayin sun zo da daman gaske kan babura su ka lalata na’urar sadarwa ta MTN don katse hanyar da za a ji labari don kawo dauki.

Sojojin da ke Zurmi su ka sanya varayin su ka janye da komawa daji.

Wani shugaban ɓarayin mai suna Majo ya ɗauki nauyin kai harin.

‘Yan bokon arewacin Nojeriya sun rubuta wasika ga shugaba Tinubu su na buƙatar ya kaucewa raɗe-raɗin kafa sansanin Amurka ko Faransa a yankin arewa.

An samu bayanai masu nuna yiwuwar kafa sansanonin Amurka da Faransa a arewacin Nijeriya bayan rasa sansanonin su a Nijar da Mali.

Waɗanda su ka sa hannu a takardar sun haɗa da Farfesa Attahiru Jega, Auwal Musa Rafsanjani, Farfesa Jibo Ibrahim da sauran su.

Fitattun ‘yan arewan sun nuna barin a kafa sansanonin koma baya ne ga tsaro don duk inda a ka yi sansanonin ba wata riba da a ka cimma.

Ƙungiyar gwamnonin arewacin Nijeriya ta yi taro a Kaduna kan lamuran tsaro, kiuncin rayuwa da rashin kasancewa yara da dama a makaranta.

Taron ya gudana a gidan tunawa da Sir Kashim Ibrahim kamar yanda a ka saba.
Ba mamaki taron ya duba illar da har yanzu Boko Haram ke yi a arewa maso gabar da kuma barayin daji a arewa maso yamma.

Hakanan taron ƙarƙashin gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya karɓi rahoto daga koungiyar tuntuɓar juna ta arewa da kuma majalisar ƙungiyoyin arewa.

Da alamu su kuma ‘yan siyasa kan yi cacar baki ko sukar juna ne don ƙarewa ko neman madafun iko. Idan za a riƙa samun suka mai ma’ana ga siyasar da ke kan madafun iko su kuma na madafun su saurara da ɗaukar matakan gyara za a iya samun maslaha.

Mai taimakawa shugaban PDP kan sadarwa Yusuf Dingyadi ya ce ko shugaba Tinubu da mataimakin sa Kashim Shettima na zaune a Abuja ba wani tasirin da su ke yi ga kyautata rayuwar talaka.

Dingyadi na ƙarin bayani ne kan caccakar da ɗan takarar jam’iyyar Atiku Abubakar ya yi cewa shugaba Tinubu ya fice daga ƙasa a lokaci guda mataimakin sa ma ya fice tamkar an bar ƙasar ba wani mai shugabancin ta.

Duk da mataimakin shugaban Shettima ya janye tafiya da bayanin jirgin sa ya samu matsala; Dingyadi ya ce ko duk mutanen biyu sun zauna dindindin a Abuja ba wani abun kirki da za su tsinanawa talakawa.

Ai ba wa shugaba Tinubu shawara kan siyasa Ibrahim Kabir Masari ya ce har yanzu PDP ba ta farfaɗo daga kayen zaɓen 2023 ba ne.

Masari ya buƙaci PDP ta jira don gwada sahihancin adawar ta a zaven 2027.

Wannan na zuwa ne lokacin da tsadar rayuwa ke ƙara tsananta a Nijeriya.

Dattijon NEPU Hussaini Gariko ya nuna takaicin abun da ya zayyana da halin ko in kula na shugabancin Nijeriya.

Alƙaluman tsadar rayuwa sun doshi kashi 33% a Nijeriya.

Kammalawa;

Kowa ya shiga nazarin hanyoyin samar da sauƙin rayuwa da kan gidan sa zuwa aƙalla makwabtan sa. Rayuwa ta cin bulus ta wuce don haka farkawa daga barci mai nauyi na akasarin talakawa ya zama sara kan gaba.