IPAC ta zaɓi sabbin shugabanni a Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An zaɓi sabbin shugabannin Gamayyar Jam’iyyu ta ‘Inter Party Advisory Council’ (IPAC), reshen Jihar Kaduna.

An zaɓi Ahmad Tijani Mustapha ne a matsayin shugaba ba tare da hamayya ba, tare da wasu mutane takwas yayin zaɓen da aka gudanar a hedikwatar hukumar INEC ta Kaduna da yammacin ranar Litinin.

Sabon Shugaban IPACɗin, Honarabul Tijani Mustapha, shi ne shugaban jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) na jihar Kaduna.

A jawabin godiya bayan zaɓen, sabon shugaban, ya gode wa kwamitin zaɓe na IPAC, sakataren gudanarwa na INEC, ma’aikata da mambobin IPAC bisa gagarumin goyon baya da amincewar da suka nuna masa, sannan ya yi alƙawarin yin duk mai yiwuwa don tabbatar da ci gaban ƙungiyar.

Ya kuma miƙa godiyarsa ga Hamisu Dahiru Usman da sauran ma’aikatan INEC masu goyon baya da suka halarci zaɓen da kuma abokan siyasa da abokansa da ‘yan uwa.

“Ina matuƙar girmama amincewar da ku ka nuna min a yau a matsayina na Shugaban Ƙungiyar IPAC ba tare da hamayya ba. Zan yi duk abin da zan iya yi, ba don in ci amanar amincewar da ku ka nuna min ba, sai don tabbatar da ciyar da ƙungiyar gaba.

“Ina kuma ƙara nuna godiya ta a gare ku, bisa ga cikakken aminci da jajircewar da ku ka nuna, haƙiƙa mun haxu a yau domin nuna nasarar dimokuraxiyya.

Sauran mambobin da aka zaɓa sun haxa da, John Solomom Yayock na ADP a matsayin mataimakin shugaba; Hon. Adamu Idris Abubakar na SDP, Sakatare da kuma Hon. Timohey Azubike na APGA a matsayin mataimakin sakatare.

Sauran sun haxa da, tsohonɗan jarida, Musa Muhammad na AAC a matsayin sabon sakataren yaxa labarai; Hajiya Fatima Sani ta PDP a matsayin Sakatariyar Tsare-tsare; Hon. Yahaya Alhasan Marafa na APM a matsayin ma’aji; Hon. Kawu Ibrahim Yakasai na jam’iyya mai mulki ta APC a matsayin sakataren kuxi da Hon. Hassan Sani na APP a matsayin mai ba da shawara kan harkokin shari’a.

An gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali, wanda Dr Joseph Ndirang daga hedikwatar IPAC na Abuja ya gudanar.