Daga FATUHU MUSTAPHA
Ƙungiyar ‘Yan Kasuwar Fetur Masu Zaman Kansu ta Nijeriya (IPMAN), ta ce ba ta samu wata sanarwar ƙarin kuɗin fetur a hukumance ba, don haka ta buƙaci mambobinta da su yi watsi da jita-jitar da ake ta yaɗawa game da ƙarin farashin fetur.
A wata ganawa da ya yi da manema labarai a wannan Juma’ar, shugaban IPMAN reshen jihar Kano, Bashir Dan-Malam, ya bai wa mambobinsu umarnin su ci gaba da saida fetur kan farashin N163 kowace lita.
Yana mai cewa duk lokacin da aka samu ƙarin farashin mai a ƙasa, masu ruwa da tsaki na fannin za su sanar da IPMAN.
Daga nan, Dan-Malam ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su kwantar da hankulansu saboda ƙungiyarsu ba ta da niyyar tsawwala wa ‘yan ƙasa.
Ya ce sun tuntuɓi masu faɗa a ji na fannin fetur game da batun ƙarin farashin inda suka shaida musu babu wani abu kamar haka.
A ƙarshe, shugaban ƙungiyar ya jaddada cewa Hukunar Fetur ta Nijeriya (NNPC), na da wadataccen mai da za ta rarraba wa sassan ƙasa wanda a cewarsa babu buƙatar sayen mai a ɓoye.