IPOB ta ɗaukaka ƙara Kotun Ƙoli bisa ayyana ta a matsayin ƙungiyar ta’addanci

Daga BELLO A. BABAJI

Ƙungiyar ƴan ƙabilar Igbo ta Baifra (IPOB), ta ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli kan ayyana ta a matsayin ƙungiyar ta’addanci.

Hakan na zuwa ne bayan hukuncin Kotun Ɗaukaka ƙara dake Abuja na ayyana ta da ƴar ta’adda, inda lauyoyinta suka nuna rashin gamsuwa da hukuncin.

Cikin takardar ƙarar da ta shigar, IPOB ta musanta batun, wanda ta ce ya saɓa wa doka musamman sashe na 36 na kundin 1999 da ke magana akan ƴancin bayyana manufofi.

Ƙungiyar ta ce hanyoyin da aka bi wajen tabbatar mata da sunan ba su cike ƙa’idojin manyan laifuka ba, tana mai cewa an gina batutuwan ne akan zarge-zarge.

Sannan ba a yi wa mambobinta adalci ba kasancewarsu galibi ƴan ƙabilar Igbo ne wanda hakan ya kai ga nuna musu wariya waɗanda duk sun ci karo da sashe na 42 na doka, kamar yadda ta bayyana.

Haka kuma ta ce ta zaɓi cigaba da fafutukar Biafra ne la’akari da dokar ƴancin ɗan-adam da kuma dokokin da suka bada damar amfani da dokokin ƴanci ɗan-adam a mataki na Ƙasa-da-ƙasa.

Wanda ƙungiyar ta ɗaukaka ƙarar akan sa shi ne Antoni-Janar na ƙasa (AGF).