IPOB ta yi kira ga Biden kada ya saurari buƙatar Buhari

Daga UMAR M. GOMBE

Masu Fafutukar Kafa Biafra (IPOB) sun aika wa Shugaban Ƙasar Amurka, Mista Joe Biden, wasiƙa ta musamman inda suka yi kira ga gwamnatin Amurka da kada da yardar da buƙatar agajin da Shugaba Muhammadu Buhari ya nema a wajenta na ta shigo ta taya shi yaƙi da matsalar tsaron ƙasa.

A cikin wasiƙar mai ɗauke da kwanan wata 1 ga Mayu, 2021 wadda ta samu sa hannun jagoran tsegerun, Nnamdi Kanu, IPOB ta shaida wa Shugaban Amurka cewa duk wani makami da Amurka za ta saida wa Nijeriya ƙarkashin mulkin Buhari, babu abin da zai ƙara mata face ci gaba da take ‘yancin ɗan-Adam.

A cewar wani sashe na wasiƙar, “Ya Shugaban Ƙasa, yarda da ka yi da roƙon Buhari kan taimaka masa da sojoji don taya Nijeriya aiki, cikin girmamawa muna kira a gare ka da ka waiwaya ka dubi yadda Buhari ya maida Nijeriya ta zama ƙasa mafi wahalar sha’ani ga Kirista a faɗin duniya, musamman ma ga jama’ar tsohuwar Tarayyar Biafra.

“Makaman da Nijeriya ke samu daga hannun Amurka don yaƙi da Boko Haram babu abin da take yi da su sai kashewa da muzguna wa kiristocin ƙasar. Sojojin Nijeriya wanda shugabancinsu ke hannun Bafulatani kuma mai kishin Islama na da hannu cikin safarar makamai ta haramtacciyar hanya.”

Wasiƙar ta nuna cewa Amurka da ƙungiyar Amnesty International sun tabbatar da irin take ‘yancin bil’adama da gwamnatin Buhari ke yi wanda har sun wallafa rahotanninsu game da take ‘yancin mutane a Nijeriya.

Lamarin da IPOB ta ce har ya kai ga Cibiyar Harkokin Addinai ta Ƙasa da Ƙasa ta Amurka ta bada shawarar a sanya Nijeriya daga cikin jerin ƙasashen da ya kamata a sanya musu ido saboda danniyar addini.

Kazalika, wasikar ta IPOB zuwa ga Shugaba Biden ta taɓo har da batun Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Intanet na Nijeriya, Isa Pantami.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *