Iran: Amurka ba ta damu da ƙasashen Musulmi ba

Daga CMG HAUSA

Shugaban ƙasar Iran Ebrahim Raisi, ya ce ko kaɗan Amurka ba ta damu da halin da ƙasashen musulmi ke ciki ba, maimakon haka, burin ta shi ne cimma muradun ƙashin kai da tabbatar da danniya.

Shugaba Raisi ya bayyana hakan ne, yayin zantawarsa ta wayar tarho da takwaransa na Iraƙi Barham Salih a jiya Lahadi. Ya ce ƙasarsa ta tallafawa Iraƙi, a fannin wanzar da hadin kan ƙasa, da samun ‘yancin kai, da tsaro, da tabbatar da gurbin ta a matakan ƙasa da ƙasa da na shiyya, kuma tsaron Iraƙi na da matuƙar tasiri ga tsaron shiyyar su baki ɗaya.

Ya ce “Alaƙar ‘yan uwantaka da abokantaka tsakanin Iran da Iraƙi, ta wuce batun maƙwaftaka kadai”.

A nasa ɓangare kuwa, shugaban Iraƙi cewa ya yi, akwai buƙatar inganta haɗin gwiwar kasashen biyu, domin shawo kan ƙalubalolin dake addabar yankin, musamman bisa la’akari da manyan buƙatun samar da daidaito da tsaron yankin.

Shugaba Barham Salih ya kara da cewa, ana iya shawo kan tashe tashen hankula da shiyyar ke fuskanta, ta hanyar haɗa ƙarfi da ƙarfe tsakanin ƙasashen dake ciki, ba tare da buƙatar tsoma bakin ƙasashen waje ba.

Fassarawa: Saminu