Dakarun juyin juya halin Iran, sun yi barazanar kai ƙarin wasu hare-hare kan Isra’ila idan ta mayar da martini kan harin makamai masu linzami da Iran ta kai mata, wanda ke zuwa bayan da Amurka ta ce tana tattaunawa kan matakin mayar da martini, inda ta ce Tehran ta kwana da shirin amsar sakamakon abinda ta aikata.
A wata sanarwa da rundunar dakarun juyin juya halin Iran ta fitar, ta ce harin na Iran martani ne game da kisan jagoran ƙungiyar Hamas Isma’il Haniyeh, da Isra’ila ta yi a wani hari da ta kai birnin Tehran a watan Yulin wannan shekarar.
Iran ta ce harin makamai masu linzami da ta kai Isra’ila, shi ne mafi girma da ta taɓa kai wa ƙasar, wanda ya ƙara haifar da fargabar ɓarkewar yaki a yankin Gabas ta tsakiya.
Rundunar sojojin Iran ta yi gargaɗin cewa, duk wata ƙasa da ta yi yunƙurin taimaka wa Isra’ila kai tsaye, za ta ɗanɗana kudarta.
A wata ganawa da aka yi da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi a kafar Talabijin ɗin ƙasar, ya ce Tehran ta gargadi Amurka game da tsoma baki bayan harin da ta kai kan Isra’ila.
Abbas ya ce sun miƙa wa Amurka saƙon ne ta ofishin jakadancin ƙasar Switzerland da ke Tehran.
Bayan wannan hari, mutane da dama ne suka taru a biranen Tehran da Beirut da Baghdad da Gabar Yammacin kogin Jordan da kuma Gaza, inda suke murna ta hanyar daga tutocin Hezbollah da Lebanon da kuma Iran.
Tuni dai ƙasashen Amurka da Spain da Jamus da Faransa da Birtaniya da Japan suka yi Allah wadai da harin na Iran kan Isra’ila, inda Spain da Jamus ke buƙatar kawo ƙarshen rikicin.
Sai dai har yanzu ana ci gaba da gwabza rikici tsakanin Isra’ila da Hezbollah a iyakar Lebanon, inda ƙungiyar Hezbollah ta ce ta yi arangama da sojojin Isra’ila da suka yi ƙoƙarin kutsawa cikin ƙasar Lebanon ta ƙasa, tare da kai hari kan sojojin Isra’ila da ke kan iyakar ƙasar.
A wata sanarwa da ta fitar a safiyar Larabar da ta gabata, Hezbollah ta ce ta yi amfani da rokoki da makaman atilari wajen kai wa wasu sansanonin Isra’ila hari. RFI.