Iran ta yanke wa Alireza Akbari hukuncin kisa bisa laifin zagon-ƙasa

Kakakin Hukumar Shari’ar Ƙasar Iran ya yanke hukuncin kisa kan wani mutum da aka samu da laifin aikata leƙen asiri, kamar yadda hukumar shari’a ta sanar a ranar Laraba da ta gabata.

Hukumar ta yankewa Alireza Akbari hukuncin kisa bisa laifin cin hanci da rashawa a doron ƙasa da kuma zagon ƙasa ga tsaron ƙasar saboda yada bayanan sirri suka tabbatar.

Har wa yau, ba ta bayar da cikakken bayani kan ranar da aka kama shi da kuma yanke irin ba, wanda kotun koli ta tabbatar da hakan.

A farkon watan Janairu, an zartar da hukuncin kisa ga wasu Iraniyawa huɗu bayan da aka same su da da aikata kisa saboda ‘haɗin kai’ da Isra’ila.

Iran ta sanar da kama wasu jami’ai da ake zargi da aikata laifukan leƙen asiri na ƙasar waje ciki har da Isra’ila.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *