Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Fadar Shugaban Amurka ta White House ta ce Isra’ila ta amince da tsagaita wuta na tsawon sa’o’i huɗu a kowace rana a hare-haren da ta ke kai wa Hamas a arewacin Gaza daga ranar Alhamis, kamar yadda gwamnatin Biden ta ce ta samar da wata hanya ga fararen hula ta ficewa daga Gaza.
Shugaban Amurka Joe Biden ya buƙaci Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da ya kafa tsagaita buɗe wuta yayin kiran ranar Litinin.
Kakakin Kwamitin Tsaron Amurka John Kirby ya ce za a sanar da tsagaita buɗe wuta na farko a ranar Alhamis, kuma Isra’ilawa sun ƙuduri aniyar sanar tsagaitawar na sa’o’i huɗu aƙalla a kowace rana.
Isra’ila, inji shi, ta kuma buɗe wata hanya ta biyu ga fararen hula da su ƙaurace wa yankunan da a halin yanzu sojojinta ke kaiwa Hamas hari.
Biden ya kuma shaida wa manema labarai cewa ya nemi Isra’ilawa da su dakata fiye da kwanaki uku a tattaunawar da ake yi kan sakin wasu mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su, kodayake ya ce babu yuwuwar tsagaita buɗe wuta.
Ma’aikatar lafiya ta Falasɗinawa ta sanar a ranar Alhamis ɗin da ta gabata cewa har yanzu sojojin Isra’ila na kai hari a Jenin da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan da suka mamaye.