Itace tun yana ɗanye ake tanƙwara shi (2)

Mu ɗora inda muka tsaya a makon jiya.

Daga SADIYA GARBA YAKASAI

Yana da kyau mu kula da irin abokan da yaran mu ke mu’amala da su. A yanayi na rayuwa, bai kamata mu sa wa yara ido suna mu’amala da kowa ba. Yana da kyau uwa ta la}anci wa yaranta ke kulawa. Da zarar kin ga yanayin yaran da yaranki ke harkar da su, to mataki na bincike za ki fara ɗauka.

Idan ki ka bari yaron ki ko yarinyar ki na kai wa dare a waje ko ƙaryan biki ko zuwa fati, to ki shirya rugujewar rayuwar ɗan ki ko ɗiyar ki. Dole ki ba ta lokacin fita da dawowa. Hakan ma ga namijin.

Barin yara su ɗau lokaci a waje, babban hatsari ne gaskiya. Idan da hali a haɗa su da wanda aka san babba ne. A cikin gida ma yara na fitina balle waje?

Waya:
ita ma yanzu ta fi mutum hatsari. Tana yin tasiri gurin ruguza rayuwar yara. Muddin za a ɗau waya sukutum a ba wa yaro da bai gaza shekara 20 ba, to iyaye da kanku kuka rusa rayuwa a gidanku, don a yanzu waya ba ƙaramar shu’umar aba ba ce. Da ita yara ke haɗa gurin zuwa, da ita yara ke ganin abun da bai dace su gani ba, a cikin ta dai wayar za a dama wa ɗanki ko ‘yar ki tafarkin lalacewa. Manya ma ba su tsira ba balle yara.

Don Allah iyaye mu yi haƙurin hana yara wayoyi masu tsada. Duk wasu ayyukan assha yanzu ta ciki suke faruwa. Don haka ba ƙaramin taka rawa waya ke yi ba gurin gurɓa ta tarbiyyar yaranmu, duba da rayuwar su da ƙwaƙwalwar su tana buƙatar abu mai kyau ba na banza ba. Akwai lokacin da ya kamata a ba su; lokacin sun girma sun san ciwon kan su. Amma yanzu yaro ɗan shekara 10 a ɗauki waya a ba shi, to don Allah meye ake tsammanin ba zai faru ba?
Allah sa mu gane gaskiya.

Shaye-shaye:
Abu na gaba da ke addabar al’umma shine shaye-shaye. Ya zama matsala a rayuwa al’umma kar ma a ce yara yanzu, har manya mata da maza duk rayuwar ake yi. Matan aure ma ba a bar su a baya ba; su ma abun da suke kenan. Ya ilahil alamu a ina za mu kai wannan matsalar? Babu kunya za ka ga mace na shan ganye ko siraf kala-kala. Ina za mu kai wannan abun? ‘Yan mata na yi, su na bin kulab-kulab yanzu ya fi komai lalata mana matasa. Sai addu’a da sa ido, don Wallahi yara suna yaudarar iyaye da sunan biki ko zuwa ƙarin karatu. To, ba fa can ɗin wasu su ke zuwa ba; kulab suke zuwa da abokansa. Idan uwa za ta duba jakar yarinyarta ko yaronta, shakka babu za ta yarda kayan ciki na canjawa. Wannan ba ƙaramar illa ba ne. Wallahi iyaye muna cikin masifu, kuma idan ba mu sa ido ba, to mu na ji, mu na gani za mu yi wa yaranmu babbar illa.

Sutura:
Yanayin sutura (kaya) da suke sawa su ma sun taka rawa wajen gurɓacewar yaran mu. Matsatsun kaya ko saka ‘English wares’ su ma sun taka rawa wajen rugujewar rayuwar su. Yana da kyau uwa ta sa ido tun wajen zaɓa wa yaranta kayan da ya kamata.

Kayan mutunci ya kamata kowacce uwa ta koya wa yaranta sawa, ba waɗanda suka saɓa wa addini da al’ada ba. Da zarar yaron ka ya fara canja kayan da suka zame miki baƙo, to ku yi gaggawar ɗaukan mataki tun kafin lokaci ya ƙure.

Son uwa:
Yanzu fa son da uwa ke ɗorawa kan ɗanta ba ƙaramin taimakawa ga rushewar rayuwa yake ba, don wannan fatan shine mugun abu a rayuwar ɗanka.

Amana da yarda:
Duba da canjin rayuwa da muka tsinci kanmu na rashin amana da yarda shi ma ya taimaka wa rayuwar mu shiga ƙunci. Yarda ta yi ƙaranci a wannan rayuwa, saboda wanda ka yarda da shi yanzu shi zai cuce ka ko a ha]a baki da shi a cuce ka. Don haka a yanzu yana da kyau ƙwarai da gaske ka san da wa ma ’ya’yanka ke mu’amala. Duk yadda kaso da ka kare kanka sai ka samu mai ƙoƙarin ganin bayanka. Yana da kyau don Allah mu san da wa muke mu’amala ta sirri, don yanzu babu wannan. Komai ya ƙare, gwara ka bar wa kanka abunka, ka yi wa kanka maganin abun da ya dame ka.

Rainon yara ƙanana:
Kula da yara ƙanana ya zama wajibi mu iyaye mu san wa mu ke ba wa kula da su; babu ɗan uwa ko maƙoci ko mai gadi. Ga shi nan yanzu yadda ake wa yara ƙanana fyaɗe, babu tausayi, ba imani. Wannan ɗabi’a ta dabbobi da ta shigo rayuwar yaranmu, ba ƙaramin tagayyara rayuwar su ta ke yi ba, kuma duk sakaci ne na iyaye da rashin kulawa.

Abun da uwa ya kamata ta yi, shi za ta ba wa mai aiki ya yi. Kin saki ɗan ki ko ɗiyar ki ga mutum baligi kuma wanda ba ki san mene ne halinsa ba, sai abu ya faru ki zo ki na kuka da ciwon danasani.

Mu tara da ku a sati na gaba, don jin me mu ka samo muku kan kula da tarbiyyar yaran mu.