Itace tun yana ɗanye ake tanƙwara shi (3)

Ci gaba daga makon jiya.

Daga BILKISU YUSUF ALI

A yau ma ga mu a cikin filin naku mai albarka na Tarbiyya, kamar yadda mu ka saba a kowane mako.

Za mu ɗora daga inda muka tsaya a makon jiya, amma kafin nan Ina so na daɗa yi wa iyaye nasiha akan rayuwar yaransu. Ita fa rayuwar nan dole sai an yi haƙuri an ajiye son zuciya an kuma dage da tilasta wa yara su san rayuwa.

Duba da yadda komai ya kacacame mana iyaye, eh mana yanzu uwa ke tsoron ɗan da ta haifa a cikinta! Ƙiri-ƙiri uwa za ta yi wa ɗan cikin ta biyayya kawai gudun ɓacin ran ɗanta; ya ilahil alamina ta yaya uwa za ta sakar wa ɗa ragamar rayuwarsa, don kawai kafa ya yi fushi?

To, wallahi ba ƙaramin rugurguza rayuwar ɗanki ko ɗiyarki ki ka yi ba. Daga lokacin da mu ka danganta yaro da ba shi duk abinda ya ke so daga lokacin daga ke har shi ku na cikin rayuwar nadama a gaba.

Yana da kyau ka ja ɗanka jiki, ba don komai ba sai don ya shaƙu da ke, ya kuma zamo marar tsoron faɗa miki duk abun da ke samun sa. Daga sanda ki ka nuna masa gazawarki ta rashin sa ido kan rayuwarsa, to daga sannan kin sakar masa lalacewa. Shi ya sa Bahaushe ya ce, ka so naka, duniya ta ƙi shi, ka ƙi naka, duniya ta so shi.
Baya haka kuma, mu duba yanayi na rayuwa; shi yaro bai san zuru ba. Dole fa sai ka tanka! Muddin ki ka nuna masa ba komai, to, haka zai yi ta tafiya. Matsala yanzu da ke samun mu su ne;
Fyaɗe 
Shaye-shaye
Yawon kulob (club)
Karuwanci a ɓoye
Soyayyar waya
Kallace-kallace
Sace-sace
Rashin aikin yi
Daba
Harƙallar siyasa.

Waɗannan abubuwa da na zamo sun yi matuƙar tasiri da ba da gudunmowar rushewar yaranmu, kuma za mu dauki ɗaya bayan ɗaya mu yi magana a kai.


Ba za mu gane illar barin yara sakaka ba da muka yi ba, sai lokaci ya ƙure. Shi ya sa da zarar hakan ya ɗauko hanyar faruwa a yi ƙoƙarin magance faruwar ta hanyar lallashi ba faɗa ba. Yawan fa]a ga yara na daɗa kangarar da zuciyarsu.

Akwai matsala da ya kamata iyaye mu magance ta, wacce ga ta nan muna ta fuskantar ta, amma sai ci ta ke yi kamar wutar daji. Wannan matsala kuwa ita ce, mutuwar auren yara ƙanana. A yi soyayya a waje kamar ba za ka mutu ba, amma ana auren bai rufa shekara ba zai mutu.

To, mu kan rasa dalilin faruwar hakan, sai dai mu kwatanta cewa ba a gina auren cikin amana da dubayyar mazan ko matan kowanne ɓangare. Kowa yana da laifi, sannan kuma iyaye ma suna ba da damar ruguje auren ta hanyar rashin bincike.

Da zarar yara sun ce su na so, shikenan; babu sanin meye sana’ar yaron, me ya ke yi aiki ko kasuwanci, a’a, kawai daga ta kawo shi kamar da ma neman kai mu ke da yaran sai a tashi aure. Wani ma bai san ciwon kansa ba, shi ma yana buƙatar a kula da shi a gida kawai zai shagwargwaɓe wai shi aure yake so. Uwa da uba, saboda so, sai a mara ma sa baya ya auri yarinya.

Ita ma ba kulawar iyayen ta sai kawai a ba ta shi ba tare da an lura da rashin cancantarsu ba; kawai ana duba soyayyarsu da kuma tilasta wa zuciya, don kada a ce yarinyarsu ta rasa miji da wuri. Daga shiga matsaloli masu girman gaske za su fara fuskantar kansu, shikenan daga nan kuma sai saki ya biyo.

Iyaye ke da laifi, ba yara ba. A nawa hangen uwa ke da alhakin sa wa ɗiyarta ido ta san meye ma auren kansa. Ba ki karantar da ita daɗi da rashinsa ba da fuskantar da ita ƙalubalen da ke cikin rayuwar aure ba; kawai akai ta, sai ta je ta ga abun ba haka ba ne. Daga baya sai fitina ta ɓullo, sai kuma rabuwa.

Yana da kyau iyaye su riƙa koyawa yaransu rayuwar aure da yadda ya ke gudun tadda abun da ba su saba gani ba. Ba laifi ba ne don uwa ta koya wa yaranta yanayin rayuwar aure da bambanci da rayuwar gaban iyaye. Tsadar rayuwar aure ta haɗa da yawaitar lallacewar aure.

Za mu tsaya a nan sai zuwa sati mai zuwa, don jin ci gaban wannan a cikin filin naku mai albarka na Tarbiyya. Wasallam!