Iyalan Abacha sun magantu kan ikirarin IBB game da soke zaɓen June 12

Daga BELLO A. BABAJI

Iyalan marigayi tsohon shugaban mulkin soji, Janar Sani Abacha, sun mayar da martani kan kalaman Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) na cewa Abacha ne ke da alhakin soke zaɓen Shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yulin 1993.

A littafinsa da ya fitar a kwanan nan mai suna ‘A journey in Service’, IBB ya yi da-na-sanin soke zaɓen, tare da tabbatar da ɗan takarar jam’iyyar SDP, wato MKO Abiola a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

A lokacin da ya ke bayyana yadda tarihin lamarin ya kasance, IBB ya ɗora wa sojoji a ƙarƙashin jagorancin Abacha laifi, wanda a lokacin kuma shi ne shugaban jami’an sojoji, ya na mai ce an soke zaɓen ne ba tare da izininsa ba.

A yayin tsokaci game da batun a wata takarda da ke ɗauke da sanya hannunsa, ɗan Abacha, Ahmad Abacha, ya ce iyalan sun yi watsi da kalaman na IBB, da cewa a lokacin da aka soke zaɓen, Abacha ba shi ne shugaban ƙasa ko babban mai bada umarni a Nijeriya ba.

Sun zargi IBB da ƙoƙarin jirkita bayanan gaskiya da tarihi ya nuna da ɗora laifin wani akan wani.

Iyalan sun kuma yi kira ga ƴan Nijeriya da su guji ɗaukar maganganun da ke ƙoƙarin sauya tunaninsu don wata manufa ta siyasa ko ta kai-da-kai.

Sun ƙara da cewa, ba zai yiwu a rushe kyakkyawan tarihin da mahaifin nasu ya bari ba da zantuƙa marasa tushe tare da yin rufa-rufa ga asalin waɗanda suka aikata laifin ba.

Kazalika, sun yi tir da littafin kan kauce wa bada bayanai na gaskiya game da al’amurran da suka faru a baya.