Iyalan waɗanda aka sace a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun yi zanga-zanga

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Iyalan waɗanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna ranar 28 ga Maris, 2022 sun gudanar da zanga-zangar nuna damuwa da kuma kira ga Gwamnatin Tarayya ta yi ƙoƙarin kuɓutar da iyalan nasu daga hannun ‘yan ta’addar.

Iyalan na cikin damuwa sosai kan kasa ceto ‘yan uwan nasu.
‘Yan uwa da iyalan waɗanda aka sace a jirgin ƙasan sun yi zanga-zangar lumana a titunan Kaduna ranar Litinin domin nuna damuwarsu kan rashin ceto ko sakin waɗanda aka sacen.

Haka kuma a Abuja ma babban birnin Nijeriya, wasu iyalai da ‘yan uwan waɗanda aka sacen sun gudanar da taron manema labarai a kan lamarin.

A ranar 28 ga watan Maris ne, wasu ‘yan bindiga suka tayar da bam a kan layin dogo na jirgin, sannan kuma suka buɗe wa jirgin da ke cike da fasinjoji wuta, inda suka hallaka wasu sannan suka yi awon gaba da wasu.

Daga ranar Litinin ɗin makon nan, kwana 42 kenan bayan harin har yanzu ba a sako waɗanda aka sace ɗin ba, inda bayanai suka nuna cewa waɗanda suka sace su sun gabatar wa da gwamnatin ƙasar wasu buƙatu kafin su saki mutanen.

Hukumomin Nijeriya na ɗora alhakin harin a kan ‘yan ƙungiyar Boko Haram.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *