Iyaye su ba wa ‘ya’yansu damar zaɓar abinda suke son zama a rayuwa – Hauwa Mustapha Babura

“Shelanta sakamakon jarrabawa na ɗaya daga cikin abinda ke sa ƙiyayyar karatu ga yara”

(Ci gaba daga satin da ya gabata)

Daga ABUBAKAR M. TAHIR

MANHAJA: A ɓangare ɗaya, al’ummar ƙasarmu Nijeriya suna da sha’awar kwaikwayo tare da ɗaukar al’adun turawa. Shin kina ganin idan hakan ya ƙara yawaita zai taimaka wurin rage matsalolin da ake fama da su a ƙasar nan?

HAJIYA HAUWA: To a gaskiya wanna wani abu ne wanda yana buƙatar al’ummar ƙasarmu musamman matasa su rinqa kulawa sosai da tsarin da zasu koya a rayuwar turawa. Sau dayawa suna zavar ɗabi’un da ya yi masu daɗi ne su mayar nasu, shi ya sa yawanci za ka ga cewa, yaranmu da ke zaune a irin ƙasashen, suna wasu ɗabi’u waɗanda idan ka yi duba al’adu da ɗabi’u a Ƙasar Hausa za kagan su a matsayin cin mutunci ko rashin kunya, wanda su a can ba wani abu ba ne a wurin su.

Kuma hakan zai yiwu ne idan iyaye ba su koyar da ‘ya’yansu muhimmancin al’adunsu da kuma sanar da su waɗanda ba su sani ba. Ko a can ƙasashen, za ka ga sun ware wurare da dama da suke zuba kayan al’adu daban-daban, musamman ma waɗanda suka jiɓince su.

Rashin kulawa da al’adunmu ne ke sa muna kallon na turawa a matsayin makwafi. Lallai hakan ba daidai ba ne. Ya kamata a ce kowane yaro ya san asalinsa, ya san yadda iyayensa suka gaji al’adunsu tare da ƙawata masa su. Kuma iyaye su rinƙa ƙawatawa ‘ya’yansu sanya kayan gargajiya tare da dasa masu yin alfahari da tufan nasu. Su koya masu cin abincinmu na gida, kwalliya irin ta mu da makamantan su.

Rashin sanin muhimmancin taka al’ada tare da tilastawa kai dole sai ka yi ta wani zai iya sa ka a matsaloli da dama, ciki har da jinya ta ƙwaƙwalwa, domin kowa da yadda Allah Ya yi shi, da kuma irin abinda ya amimcewa jikinshi ya karva ba tare da gardama ba.

Abin takaici ko kaɗan ba ma alfahari da kasancewar mu ‘yan Afrika. Ko ta ɓangaren turanci iyaye sun fi so ‘ya’yansu su yi irin na bature, to sannan ne za su amince da sun iya.

Idan mun tarbiyyartar da ‘ya’yanmu bisa turbar namu ɗabi’u da al’adu, za ka ga duk inda suka samu kansu, zai yi wuya su zubar su ɗauki na wa’ansu.

Haka kuma ya kamata iyaye su sani, yawan takurawa yaro ba tarbiyya ba ce, domin hanya ce ta daƙushe wa yaro ƙwaƙwalwa. Kuma idan an lura da yaro na da kaifin basira, kada a sake shi ya ji da kansa don yana saurin ganewa, sau da yawa yaro zai taso da kaifin basira, amma rashin kulawar iyaye sai a wayi gari ƙwawalwar ta disashe.

Don haka kwaikwayon al’ada da wasu ɗabi’u na turawa ba zai kaimu ga tudun na tsira, domin ko mu nan da muke rayuwa cikin turawa, akwai wasu lokuta da yaro zai yi wani abu mu gan shi a matsayin rashin tarbiyya, don mu ba haka iyayenmu suka koyar da mu ba.

Koda za mu ba su tarbiyya bisa al’adun bature, to mu zaɓo masu kyau da ya kamata a ce muna da su, mu yi koyi, kamar rashin takurawa yaro sosai tare da ba wa yara damar zavar abinda suke ao su zama a rayuwa.

Wane kira ki ke da shi ga malamai wajen inganta ilimi karan kansa?

To a gaskiya ya kamata malamai su rinƙa sanin cewa tarbiyyar yara amana ce a kansu wanda kuma Allah zai tambaye su kanta. Babu buƙatar malami ya rinƙa nunawa ɗalibansa bambanci. Misali wannan ya fi ƙoƙari ko wannan daƙiƙi ne, wannan ba daidai ba ne.

Kamata ya yi har a manyan makarantu ya zamana akwai ‘privacy’, inda ɗalibi na da sirri akan komai nasa, ciki kuwa har da sakamakon jarrabawarsa. Idan ya kasance yaro yana kallon abokin karatunsa ya fi shi, ko an kafa sakamakon ya yi na qarshe zai iya saka masa raɗaɗi da ƙiyayyar karatu da makaranta bakiɗaya.

Wannan zai sa idan aka sirrinta, yaro zai ji ya yi ƙoƙari koda kuwa bai yi ba, don yana kallon ƙila ma ya fi wane abokinshi. Kuma idan ya yi na ƙarshe, zai fi jin ƙarfin dagewa ya yi karatu don kar ya sake zama na ƙarshe har sauran ɗalibai su gane.

Amma da zarar yaro ya lura wane ya fi shi ƙoƙari har malaminsu ya fi ji da shi, yana nuna masa fifiko, to zai dinga jin shi ba shi da wani amfani, har ta kai ya fidda rai daga karatun. Don haka dole malamai su rinƙa kulawa sosai da yanayin yadda za su yi mu’amala da yara ɗalibansu.

Wane kira ki ke da shi ga gwamnati wajen inganta harkar ilimi?

To gaskiya Ina da kira musamman ga gwamnati wajen tattalin matasa tunda sun fi kowa yawa ga kuma rashin abin yi. Babu dole a ce yaro ya je ya yi karatu tsawon shekaru, amma ya dawo ya rasa abin yi, saboda gwamnati ba a shirye ta ke ta inganta rayuwarsa ba.

Wannan ke sa da yawa su faɗa munayen hallaya a ƙoƙarin su na bayyana ɓacin ransu, kamar shaye-shaye, yiwa yara ƙanana fyaɗe, sata da sauran su. Duk mai ya kai su? Rashin shirin gwamnati na inganta rayuwarsu.

Haka kuma ta ɓangaren ilimi, ya kamata a ce gwamnati ta dinga karɓar shawarwarin masana na ciki da wajen ƙasa kan sha’anin inganta harkar ilimi, ta kuma yi aiki da su wurin ganin ta inganta ilimin don amfanin yara masu tasowa. Saboda kusan gabaɗaya ‘system’ ɗin na buƙatar ayi masa garan-bawul, wanda masana su ne za su bada hanyoyin da dabarun da za a bi wajen ganin an inganta harkar ilimi a ƙasarmu.

Mun gode da bamu lokaci.

Ni ma na gode ƙwarai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *