Daga SANUSI MUHAMMAD Gusau
Ƙungiyar iyayen ɗaliban da ke karatu a Jami’ar Ƙasa da Ƙasa da ke Ƙasar Cyprus Yan asalin jihar Zamfara, sunyi kira ga gwamnatin jihar Zamfara da ta gaggauta duba halin da ‘ya’yansu 88 ke ciki don ceto su daga halin kuncin rayuwa da suke a ciki a Ƙasar ta Cyprus.
Ɗaliban suna karatun kwasa-kwasai daban-daban ne a Ƙasar Cyprus ƙarƙashin Jami’ar Ƙasa da Ƙasa Nicosia waɗanda gwamnatin Jihar ta tura tun gwamnatin da ta gabata ta Ƙaramin ministan tsaro Bello Muhammad Matawalle.
Shugaban Ƙungiyar Ambasada, Ibrahim Tudu ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai a Gusau yau Laraba.
A cewar shi, ɗaliban sun shafe sama da shekaru 4 a Ƙasar Cyprus, wasu kuma suna gab da kammala karatunsu, wasu kuma sun kammala karatu a bara amma saboda sake jarabawar zango da suka samu sakamakon rashin biyan kuɗin makaranta da gwamnati ta yi don haka har yanzu ba su iya gama karatun ba.
“Wannan taron manema labarai ya zama dole, domin jan hankalin mai girma Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal don ceto rayukan waɗannan ɗalibai ba tare da ɓata lokaci ba”. Yace
“Ɗaliban mu 88 suna fuskantar matsaloli da dama da suka shafi rashin ciyarwa, masauki, alawus alawus, kare lafiyarsu, karatunsu da kuma yanayin rashin lafiya a halin da muke ciki a sakamakon rashin biyan kuɗin rajista, kuɗin karatu da alawus ɗin su”.
“Mun amince da cewa wasu kuɗaɗe da gwamnatin yanzu ta biya wa cibiyar da ke ƙasar Cyprus Naira miliyan 224 amma har yanzu bashin yana ƙaruwa wanda hakan ya haifar da mummunar alaƙa tsakanin mahukuntan makarantar da ɗaliban mu, wanda hakan ke kawo illa ga karatun ɗaliban kasancewar duk wata yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) har yanzu bata tabbata ba”.
“Ɗaliban yanzu haka suna cikin tsananin rayuwa da haɗari da kuma cin karo da ƙunci da yawa kuma an kore su daga ɗakunan kwanan ɗalibai na makarantar, suna zaune a masallatai da gidajen haya inda ake cin zarafinsu saboda rashin biyan kuɗin haya”.
A cewarsa, mata goma daga cikin ɗaliban suna cikin mawuyacin hali da matsaloli da dama a rayuwar su a Ƙasar ta Cyprus.
Ya kuma kara da cewa Fasfo na ƙasa da ƙasa na ɗaliban da kuma takardar samun izinin zama a Ƙasar ta Cyprus na ɗaliban tuni ya ƙare kuma suna fuskantar barazanar kama su daga mahukuntan Ƙasar wanda zai kai ga tsare su, ɗauri da kuma fitar da su zuwa gida Nigeria in har gwamnatin jihar bata ɗauki matakin gaggawa ba game da lamarin.
Haka zalika Ambasada Ibrahim Tudu ya koka da yadda ɗaliban Zamfara ba sa samun kuɗaɗen alawus-alawus na wata-wata wanda za su yi amfani da su wajen sayen ruwan sha da sabulun wanka da wanki da sauran abubuwan buƙatu na rayuwa tsawon shekara biyu kenan a halin yanzu.
“Kamar yadda nake magana a yanzu, iyayen ɗaliban suke aikawa da kuɗi ga ‘ya’yansu maza da mata yayin da su kansu iyayen komai nasu ya ƙare kuma a zahiri ba za su iya ɗorewa ba sannan kuma ita kanta gwamnatin Jihar Zamfara sun san da matsalar “.
Ambasada Tudu ya bayyana cewa ƙiyasin kuɗin bashin da Jami’ar Ƙasa da Ƙasa da ke Ƙasar Cyprus ke bin jihar ta Zamfara zai iya kaiwa Naira Biliyan ɗaya ko sama da haka, lura da cewa, tunda Gwamnatin da ta shuɗe itace ta kaisu bisa doka, ya zama wajibi gwamnati mai ci yanzu ta ɗauki alhakin biyan kuɗin makarantar ɗaliban.
“Ɓacin rai da wannan al’amari ya kawo Zamfara ba a taɓa ganin irinsa ba, kuma bai dace ba musamman gwamnatin nan da ta zo aikin ceto”.
A halin da ake ciki, da aka tuntuɓi kwamishinan ilimi, kimiyya da fasaha na jihar, Alhaji Wadatau Madawaki kan lamarin, ya ƙi cewa komai, yana jaddada cewa yana fama da rashin lafiya da ba zai iya tattaunawa da manema labarai ba a halin yanzu.