Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kwamitin daƙile yaɗuwar cututtukan ƙanjamau, tarin fuka da zazzaɓin cizon sauro na majalisar wakilai ta ƙasa ta yi kira ga gwamnatin tarayya kan ɗaukar matakan da suka fi dacewa domin hana jabun magungunan cizon sauro a ƙasar nan.
Shugaban kwamitin Amobi Ogah mai wakiltan jihar Abia daga jami’yyar LP ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar domin tunawa da ranar Cutar zazzaɓin cizon sauro ta duniya da aka yi ranar Lahadi.
An keɓe ranar 20 ga Agusta na kowace shekara bayan wani Bature Ronald Ross ya gano cewa macen sauro ‘Anopheline’ ne ke yaɗa cutar bayan ta ciji mutum.
Taken taron bana shi ne “Yaƙar cutar da ta fi kisan mutane a duniya wato sauro”.
Majalisar ta ce ya zama dole gwamnati ta yi gaggawar ɗaukar tsauraran matakai domin daƙile yaɗuwar cutar musamman yadda Nijeriya na daga cikin ƙasashen duniya dake da yawan mutane da cutar ke hallakawa.
“Za mu yi ƙoƙari wajen ganin an hana jabun maganin cutar sannan za mu ƙarfafa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko domin ganin sun daƙile yaɗuwar cutar a ƙasar nan.
“Adadin yawan mutanen da cutar ta kashe a Nijeriya ya kai kashi uku na mutum 619,000 da cutar ta kashe a duniya.
Ogah ya ce kwamitin a shirye yake domin haɗa hannu da ƙungiyoyi da masu ruwa da tsaki domin daƙile yaɗuwar cutar a ƙasar nan.
Ƙungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa masana kimiyyar haɗa magunguna sun haɗa maganin rigakafin zazzaɓin cizon sauro ta farko a duniya.
Shugaban WHO Tedros Ghebreyesus ya ce maganin zai taimaka wajen kare mutane musamman ƙananan yara daga kamuwa da cutar.