Jagorancin APC a Kano: Ɓangaren Shekarau ya buƙaci kaso 55 da muƙamin shugaban jam’iyya

Daga BASHIR ISAH

Da alama dai wutar rikicin jam’iyyar APC a Kano na ci gaba da ruruwa musamman ma ganin yadda tsagin tsohon gwamnan jihar, Sanata Ibrahim Shekarau, suka dake kan buƙatun da suka gabatar wa shugabancin jami’iyyar na ƙasa.

A ranar 8 ga Fabrairu ne tsagin Sanata Ibrahim Shekarau ya rubuta wa babban ofishin APC na ƙasa wasiƙa yana mai nuna rashin jin daɗinsa kan cewa an ƙi sauraron buƙatun da ya gabatar wa ofishin.

Haka nan, cikin wata wasiƙar da tsagin na Shekarau ya sake aike wa babban ofishin APC, mai ɗauke da kwanan wata 9 ga Fabrairu, wadda ta samu sa hannun Sanata Ibrahim Shekarau (APC-Kano ta Tsakiya), Sanata Barau Jibrin (APC-Kano ta Arewa), Tijjani Jobe (APC- Mazaɓar Tarayya ta D/Tofa/Rimingado), Nasiru Gabasawa (APC- Mazaɓar Tarayya ta Gezawa/Gabasawa), Haruna Dederi (APC- Mazaɓar Karaye/Rogo), Sha’aban Sharaɗa (APC- Mazaɓar Tarayya ta Kano Municipal) da kuma Shehu Dalhatu (Shugaban ƙungiyar Buhari Support Group), sun nuna cewa lallai sai dai a ba su kaso 55 na jagorancin jam’iyyar APC ta Kano.

Kazalika, sun buƙaci a janye ɗaukaka ƙarar da gwamnati ta yi game da hukuncin da wata Babbar Kotu ta yanke don kwatanta gaskiyarsu.

Tsagin na Sanata Shekarau sun ce, za su ci gaba da marta aniyyar uwar jam’iyya na kokarin samar da salama a cikin jam’iyyar a duk lokacin da jam’iyyar ta fuskanci wata matsalar cikin gida.

Tare da cewa suna da yaƙinin uwar jam’iyyar na da dukkanin damar da za ta yi hukuncin da zai ciyar da jam’iyya gaba da gyara mata zama musamman ma rehsen jihar Kano

Sai dai duk da wannan, ɓangaren Shekarau sun nuna cewa suna nan kan bakansu dangane buƙatar kaso 55 da suka nemi a ba su na shugabancin jami’iyyar APC a Kano, kuma ya zamana su ke da mukamin shugaban jami’yya sannan ɓangaren Gwamna Ganduje ya samu kashi 45.

Haka nan, sun buƙaci duk wani kwamitin sasantawar da za a kafa kada ya zama a ƙarƙashin kulawar Gwamna Gnduje.

Kazalika, sun buƙaci dole ɓangaren Ganduje ya janye duk wata ɗaukaka ƙarar da yi domin haka ya zama shaidar lallai ana son sulhunta tsakani da gaskiya.

Ɓangaren Sanata Shekarau sun yi kira ga uwar jam’iyya da ta yi nazari mai zurfi kan matsalolin da suka addabi APC a Kano sannan ta yi abin da ya dace don hana jirgin APC na Kano kifewa a cikin kogi.