Jakadan Ƙasar Sin ya bayyana damuwa kan yadda ake nuna bambanci ga ‘yan ƙananan ƙabilu yayin da ake aiwatar da doka akan wasu ƙasashe

Daga CMG HAUSA

Jiya Talata 4 ga wata, an yi babbar muharawa dangane da batutuwan wariyar launin fata, da nuna kiyayya ga baki, da rashin haƙuri, a yayin taron kwamitin kare haƙƙin ɗan Adam na MƊD karo na 51.

A yayin muhawarar, zaunannen wakilin ƙasar Sin a ofishin MƊD a Geneva da sauran ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa a ƙasar Switzerland Jakada Chen Xu, ya yi jawabi a madadin ƙasashen da ke da ra’ayi kusan iri ɗaya da na ƙasar Sin, inda ya nuna matuƙar damuwa kan yadda ake nuna bambanci, ga ‘yan ƙananan ƙabilu, yayin da ake aiwatar da doka a wasu ƙasashe, ya kuma buƙaci ƙasashe masu ruwa da tsaki da su kalli kansu yadda ya kamata, a fannin mummunar matsalar wariyar launin fata, su yi cikakken bincike, da kyautata hukumominsu, da dokokinsu, da manufofinsu, da matakansu masu nasaba da wariyar launin fata, a ƙoƙarin aiwatar da “sanarwa da tsarin ayyuka na Durban” yadda ya kamata.

A cikin jawabinsa, Chen Xu ya yi nuni da cewa, yadda hukumomin aiwatar da doka suke nuna bambancin launin fata, da yin amfani da ƙarfin tuwo yayin da suke aiki, sakamako ne da waɗannan ƙasashen suka samu, saboda sun daɗe suna fama da matsalar wariyar launin fata, da rashin daidaito cikin zamantakewar al’umma bisa tsari, kana matsala ce da ya zuwa yanzu ba su warware ta ba, tun bayan cinikin bayi da mulkin mallaka.

A cikin waɗannan ƙasashe, an dade ana nuna wa ‘yan asalin Afirka, da Asiya, da musulmai, da sauran ‘yan ƙananan ƙabilu bambanci, da ɗaukar su mutane marasa muhimmanci, ana kuma keta dokokinsu, kuma ko da yaushe suna fuskantar barazanar cin zarafi.

Cikin jawabinsa, Chen Xu ya yi kira ga kwamitin kare hakkin dan Adam na MƊD, da ofishin babbar jami’ar kula da haƙƙin dan Adam na MƊD, da su ƙara mai da hankali kan batutuwa masu nasaba da wariyar launin fata, da tashin hankali da aka ambato, tare da ɗaukar matakan da suka wajaba na magance hakan.

Mai fassara: Tasallah Yuan