Jakadan Morocco: Morocco tana martaba “manufar Sin ɗaya tak a duniya”

Daga CMG HAUSA

A kwanakin baya ne, jakadan ƙasar Morocco dake nan ƙasar Sin Aziz Mekouar, ya nanata yadda masarautar ƙasarsa take martaba “manufar Sin ɗaya tak a duniya”, a matsayin tushen dangantakar dake tsakanin ƙasashen abokan juna.

Mekouar ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin ƙasar Moroccon dake nan ƙasar Sin ya fitar game da batun yankin Taiwan na ƙasar Sin.

A cikin sanarwar, Mekouar ya bayyana cewa, a tsakanin ɓangarorin biyu da kuma na ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, Morocco za ta ci gaba da goyon bayan ƙasar Sin kan wannan batu, tare da jaddada matsayinta.

Yana mai cewa, matsayin masarautar ya shafi mutunta ikon mulkin ƙasa, da cikakkun yankunanta, da rashin tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran ƙasashe.

Ya ƙara da cewa, Morocco ta yaba da goyon baya da matsayin ƙasashe abokai na goyon bayan kare yankinta.

Dangane da dangantakar da ke tsakanin ƙasar Morocco da ƙasar Sin kuwa, jakadan ya bayyana cewa, ƙasarsa tana mai da hankali sosai, kan dangantakar dake tsakanin ƙasashen biyu, yana mai jaddada cewa, ƙasashen biyu sun ƙuduri aniyar ƙarfafa haɗin gwiwarsu a fannoni daban daban.

Jakada Mekouar ya nuna cewa, shawarar “ziri daya da hanya daya (BRI)” ta buɗe sabbin damammaki na kasuwanci da zuba jari, da karin damammaki da suka dace da sabon tsarin masarautar game da raya ƙasa.

Fassarawar Ibrahim

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *