Jakadan Sin dake Nijeriya ya gana da Janar Gowon

Daga CMG HAUSA

Jakadan ƙasar Sin a tarayyar Najeriya Cui Jianchun, ya gana da tsohon shugaban gwamnatin sojan ƙasar Yakubu Gowon, wanda ya taba ba da gagarumar gudummowa ga ci gaban huldar diplomasiyyar tsakanin ƙasashen biyu.

Jakada Cui ya bayyana cewa, a halin yanzu, hulɗar dake tsakanin Sin da Najeriya tana gudana yadda ya kamata ƙarƙashin ƙoƙarin da gwamnatoci da al’ummomin sassan biyu suke yi, kana ƙasashen biyu suna goyon bayan juna a fannin siyasa, kuma suna taimakawa juna wajen ci gaban tattalin arziki da cinikayya. Ya ce a nan gaba, ƙasar Sin tana son hada hannu da Najeriya domin tabbatar da sakamakon da aka samu yayin taron ministoci karo na 8 na dandalin tattauna haɗin gwiwar Sin da ƙasashen Afirka, tare kuma da ciyar da hulɗar dake tsakanin sassan biyu gaba.

A nasa ɓangaren, janar Gowon ya bayyana cewa, “Kasar Sin da al’ummun Sinawa dake ƙarƙashin jagorancin JKS, sun samu babban sakamako wajen gina ƙasarsu, na taba ziyartar ƙasar Sin sau da dama a shekarun 1980 da na 1990, da idona na ga yadda ƙasar Sin ta sauya daga ƙasar aikin gona dake fama da koma baya, zuwa ƙasar masana’antu mai wadata. Ya dace ƙasashe masu tasowa kamar Najeriya su koyi fasahohin gudanar da harkokin ƙasa irin na ƙasar Sin.

Haƙiƙa a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, tarayyar Najeriya ita ma ta samu babban ci gaba a fannin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma, mun godewa ƙasar Sin saboda goyon bayan da take ba ci gaban Najeriya a fannoni daban daban.”

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa