Jakadan Sin: Wanzuwar zaman lafiya ne kariya mafi kyau ga yara a Ukraine

Daga CMG HAUSA

Wakilin ƙasar Sin ya bayyana a ranar Alhamis cewa, cimma nasarar wanzuwar zaman lafiya shi ne kariya mafi kyau ga ƙananan yara a Ukraine.


Dai Bing, mataimakin zaunannen wakilin ƙasar Sin a MƊƊ ya bayyana cewa, neman yadda za a cimma zaman lafiya shi ne kariya mafi kyau ga yara.

Tattaunawar sulhu da neman cimma matsaya su ne hanyoyi mafiya tabbaci kuma hanyoyi masu ɓullewa da za su kai ga tsagaita buɗe wuta. Ya kamata al’ummun ƙasa da ƙasa su ƙarfafa gwiwa ga Rasha da Ukraine don su amince ga komawa kan teburin tattaunawar sulhu, kuma a ci gaba da bin matakan siyasa domin mayar da zaman lafiyar, in ji wakilin na Sin.

Jakadan na Sin ya ce, sanya takunkumi ba zai kawo zaman lafiya ba, sai dai ma ya ƙara ta’azzarar rikicin da ake fama da shi, da haddasa tsananin karancin abinci, da makamashi, da haifar da karayar tattalin arzikin duniya baki ɗaya, kana lamarin zai iya yin sanadiyyar jefa ƙananan yara a fadin duniya cikin tsananin wahala.

Yaran dake rayuwa a ƙasashen da ake fama da yaƙe-yaƙe, kamar Afghanistan, da Yemen, da kusurwar Afrika, da ma yankin Sahel, suna ɗanɗana kuɗarsu sakamakon ƙarancin tallafin jin kan bil adama.

Mr. Dai ya ce, ƙasar Sin tana ƙara yin kira ga dukkan ɓangarori masu ruwa da tsaki da su shiga taitayinsu, kana su kai zuciya nesa, su guji haddasa kiyayya da kawo ɓaraka, kana su tsaya tsayin daka wajen ƙoƙarin kashe wutar rikicin Ukraine a kan lokaci, domin a samarwa yara kyakkyawar makoma mai cike da zaman lafiya da lumana.

Fassarawa: Ahmad