Daga USMAN KAROFI
A wata sanarwa da aka wallafa a shafinta na X a ranar Laraba, JAMB ta tabbatar wa da masu neman shiga jarabawar cewa za a sanar da cikakkun bayanai kan tsarin rijistar nan ba da jimawa ba.
Sanarwar ta ce: “A lura masu neman gurbin jarabawar UTME/DE na 2025! Rijista ba a fara ba tukuna. Duk da haka, za mu sanar da cikakkun bayanai nan gaba. Kuna iya samun NIN da kuma lambar waya wacce ba a taɓa amfani da ita wajen rijista ba don ƙirƙirar lambar ku ta profile kafin lokacin.”
Haka kuma, JAMB ta bayyana cewa littafin ‘The Lekki Headmaster’ na Kabir Alabi Garba ne aka amince da shi a matsayin littafin karatu don sashen Turanci na jarabawar UTME ta 2025.
Sanarwar ta ƙara da cewa: “A lura masu neman shiga jarabawar UTME na 2025! Wannan shi ne sanarwa cewa littafin The Lekki Headmaster na Kabir Alabi Garba ne aka amince da shi a matsayin littafin karatu don sashen Turanci. Za mu fitar da cikakkun bayanai kan rijistar UTME/DE nan gaba. A kasance cikin shiri don samun ƙarin bayani.”