JAMB za ta fara barin ɗalibai shiga zauren jarrabawar UTME da wayoyinsu

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Shirya Jarrabawar Neman Gurbin Karatu a Manyan Makarantu (JAMB), ta ce tana nazari kan wata sabuwar dokar da za ta bai wa masu rubuta Jarrabawar UTME damar yin amfani da wayar salula da makamancinta yayin rubuta jarrabawar.

Shugaban hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana haka a wurin taron da suka gudanar a ranar Asabar a Abuja.

A cewar Shugaban, buƙatar samar da wannan sabuwar dokar ta taso ne duba da tsadar gudanar da jarrabawar UTME a faɗin ƙasa da hukumar kan fuskanta.

Oloyede ya ƙara da cewa, hukumar JAMB ka kashe sama da Naira biliyan 1.2 wajen kimtsa cibiyar kwamfuta (CBT) da ke Jihar Kaduna don rubuta jarrabawar da kuma tanadin kwamfutocin da ɗalibai za su yi amfani da su wajen jarrabawar.

Ya ce mai yiwuwa sabuwar dokar ta amince wa ɗalibai zuwa da wayoyi da makamantansu cikin zauren rubuta jarrabawar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *