Jamhuriyar Afirka ta tsakiya (CAR) ta mayar da Bitkoyin kuɗin ƙasarta

Daga AMINA YUSUF ALI

Jamhuriyar mulki ta Afirka ta tsakiya (CAR) ita ma ta bi sahun El Salvador wajen mayar da Bitkoyin a matsayin kuɗinta na ƙasa.

Jaridar Sierra Leone Telegraph ta bayyana cewa, Afirka ta Tsakiya wacce a kwanakin baya yaƙi ya yi wa raga-raga da ita, ta ƙaddamar da Bitkoyin a matsayin kuɗin ƙasarta na halaliya wanda za a iya yin dukkan wata hada-hadar ta kuɗi, kamar cinikayya, ko harkar banki da sauransu.

Sai dai wannan mataki da ƙasar ta ɗauka ya jawo mata cece-ku ce, domin ana zargin ƙasar ta yi gaban kanta ne ba tare da tuntuɓar Babban bankin wanda shi ne cibiyar da take tafiyar da harkokin kuɗi a ƙasashen Afirka ta tsakiya ba, wanda yake a Youndé, Cameroon.

Wannan banki shi yake tafiyar da dukkan hada-hadar kuɗi a ƙasashen guda shidda da suka haɗa da, ƙasashen CAR, Cameroon, Gabon, Chadi, Equatorial Guinea da jamhuriyar Congo wanda dukkansu suna amfani da CFA franc (Saifa) a matsayin kuɗin ƙasashensu.

Har yanzu ƙasar Faransa tana da ikon juya ƙasashen Afirka guda 15, wasu daga Afirka ta Tsakiya, wasu daga Afirka ta Yamma da suke amfani da CFA Franc a matsayin kuɗin ƙasarsu. Har gobe ana zuba kuɗaɗen ƙasar a Baitul Malin Faransa.

Kasancewar waɗannan ƙasashe suna daga cikin ƙasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka ne a baya, sannan kuma har yau ita take tafiyar da harkar kuɗaɗensu, Wannan hukunci na ƙasar CAR ya zo a ba zata. Kuma ya jawo zargin cewa, wannan wani yunƙuri ne daga ƙasashen Afirka don zamewa daga wannan mulkin mallakar ta ƙasar Faranshin.

Wannan ba ya rasa nasaba da a kwanakin baya da ƙasashen Afirka masu amfani da CFA Franc suka yi yunqurin samar da wani kuɗin na bai-ɗaya a Afirka mai suna Eco.

Amma da sharaɗin ƙasar Faransa za ta cigaba da zama a matsayin masu tafiyar da harkar bankunansu. Sai dai wannan yunƙuri bai kai ga nasara ba. Duk da haka, sun zargi amfanin da suke da kuɗin Faransan a matsayin abinda yake jawo musu ci baya a tattalin arzikinsu.

Sai dai kuma a hannu guda, wasu suna ganin Bitkoyin ba zai tava ɗaukar matsayin kuɗin ba, ko ya iya taka rawar da kuɗin yake yi a rayuwar jama’a ba. Wasu suna ganin ma ya fi kama da kadara a maimakon kuɗi. Sannan hanyar hada-hadar tana buƙatar ƙwarewa a harkar na’ura mai ƙwaƙwalwa, wanda zai jawo cin lokaci da asarar dukiya da ƙarfi. Sannan adadin mutanen da suke amfani da Bitkoyin ɗin ba su da yawa ko kaɗan ballantana a ce ya zama kuɗin amfanin kowa da kowa a hukumance.

Amma ko ma dai yaya ne, ana ganin shi yanke hukuncin amfani da Bitkoyin maslaha ce ga ‘yan kasuwar jamhuriyar Afirka ta tsakiya da ‘yan siyasarsu, akwai abinda suke son cimmawa da hakan.