Jami’an tsaro a Sudan na ci gaba da gwabzawa da ma su ƙyamar mulkin Soja

Jami’an tsaro a Ƙasar Sudan sun ci gaba da fesawa ma su zanga-zanga don nuna kyamar mulkin Soja, hayaƙi mai sa ƙ kwana ɗaya bawallayan da jami’an tsaron suka kashe mutane 15.

Ma su boren da yawa suka ja daga hanyoyi da ke arewacin birnin Khartoum, kwana ɗaya bayan kisan mutane da aka samu yayin boren nuna adawa da mulkin soja.

Babban Janar Abdel Fattah al-Burhan da ke riqe da shugabancin ƙasar tun watan Aprilu 2019 da aka kifar da Gwamnatin shugaba Omar al-Bashir, ya tsare shugabannin fararen hula inda ya ayyana dokar ta-ɓaci ranar 25 ga watan Oktoba.

Matakin na sa ya yi matuƙar haifar da ruɗani da nuna rashin amincewa daga ƙasashen duniya da ke ganin Soja sun hana mulkin Demokraɗiyya.

Al-Burhan ya musanta cewa ba juyin mulki ya yi ba, amman mataki ne na gyara tsarin miƙa mulki hannun farar hula.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *