Jami’an tsaro sun tarwatsa maɓuyar ɓatagari a Akwa Ibom

Daga WAKILINMU

Rundunar haɗin gwiwa ta jami’an tsaro a jihar Akwa Ibom, ta yi nasarar tarwatsa maɓuyar wasu ɓatagari a yankin Ntak Ikot Akpan a jihar.

Sanarwar da ta fito ta hannun Daraktan Hulɗa da Jama’a na Sojoji, Brig. Gen. Mohammed Yerima, ta nuna ƙura ta lafa a yankin, yayin da kuma ‘yansanda na ci gaba da sa-ido don bai wa jama’ar yankin damar ci gaba da gudanar da harkokinsu ba tare da wani tsoro ko fargaba ba.

Yerima ya buƙaci jama’a da su kwantar da hankulansu kana su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai don samun ƙarin nasarori a kan waɗanda aka samu kawo yanzu.

Idan dai za a iya tunawa a ‘yan makonnin da suka gabata jami’an tsaro da ma ofisoshinsu sun fuskanci hare-haren ɓatagari a yankin Kudu-maso-gabas.

Musamman ma hare-haren baya-bayan nan da suka auku a jihar Imo inda ɓatagarin suka far wa gidan yarin Owerri lamarin da ya yi sanadiyar fursunoni da dama suka tsere.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *