Jami’ar Azman Kano za ta fara yin digiri a ɓangaren tuƙin jirgin sama

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Jami’ar nan mai zaman kanta mai suna Azman University da ke Kano, za ta fara yin digiri a fannin koyon tuƙin jirgin sama wanda ya ke shi ne na farko a Nijeriya da ma Afirka ta Yamma.

A zantawarta da manema labarai da ya gudana a harabar makarantar da ke ‘Yargaya da ke kan titin Wudil ranar Talata, Shugabar Jami’ar Farfesa Fatima Batulu Muktar ta bayyana cewa Jami’ar Azman ta samu sahalewar yin kwasa-kwasan tuqin jirgin sama guda biyu da suka haɗa da; Aviation Management da kuma Aviation Security.

Ta kuma ce Jami’ar Azman za ta fara karatu ne da tsangaya guda uku da suka haɗa da: Faculty of Computing and Science da Faculty of Allied health Science da kuma Faculty of Social and Management Science, inda ta ce a cikin waɗannan tsangayu uku za a gudanar da kwasa-kwasai guda 20.

“Baya ga waɗancan muhimman bayanai kwasa-kwasai tuƙin jirgin sama, za mu yi wani course mai muhimmanci wato Public Health wanda ɗai aikun jami’a ne a ƙasar nan suke yin sa, kuma mu yanzu hukumar kula da jami’o’i ta NUC ce muke jira ta zo ranar 17 ga watan Agusta da muke ciki ta duba makarantar to daga nan za ne za mu fara admissions, domin mun tanadi ɗakin gwaje-gwaje da ɗakin karatu da ofisoshi da ma ɗakunan karatun ɗalibai da sauransu,” a cewar Farfesa Fatima Batulu.

Tunda farko a jawabinsa, mu’assasin Jami’ar Dr. Abdulmanafi Yunusa Sarina wanda Alhaji Mustapha Yunusa Sarina ya wakilta ya ce bayyana cewa cikin shekara biyar da fara fafutukar kafa makarantar, ya zuwa yanzu ƙiris ya rage a fara karatu a wannan makaranta, domin mun dauki shugabannin Jami’ar an samar da kwamitin amintattu da kwamitin shura, don haka ya ce daf a ke a fara admissions sannan a karatu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *