Jami’ar Bayero ta ƙaddamar da ƙamus ɗin Hausa zuwa Ingilishi a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano 

A ranar Asabar da ta gata an ƙaddamar da sabon qamus ɗin harshen Hausa zuwa Ingilishi da ya gudana a Jami’ar Bayero ta Kano.

Littafin dai yana ɗauke da shafi 627, wanda Bature kuma masani a ɓangaren harsuna da ke Jihar Indiana ta Amurka, Paul Newman da mai ɗakinsa, Roxana Ma Newman suka wallafa, kuma maɗaba’ar Jami’ar Bayero ta buga shi.

Newman dai ya tava zama a  Kano ne tun a  shekarar 1972, inda ya  zama Darakta na farko a Cibiyar Koyar da Harsunan Nijeriya a BUK, lokacin tana Kwalejin Abdullahi Bayero.

Da ya ke ta’aliqin littafin, Shugaban Hukumar Bunƙasa Binciken Ilimi ta Nijeriya (NERDC), Farfesa Isma’il Junaidu, ya ce ƙamus ɗin shi ne irinsa mafi girma tun kusan shekarun 1930.

Ya ƙara da cewa an rubuta littafin ne ta hanyar amfani da daidaitacciyar Hausa, yayin da mawallafin littafin shi kuma yana ɗaya daga cikin masu faɗa a ji a duniya, a ɓangaren harsunan yankin Tafkin Chadi.

A jawabinsa na wakilta mawallafin littafin Paul Newman, Shugaban Makarantar Karatun Gaba da Digiri ta Jami’ar Bayero Farfesa Mustapha Ahmad Isa, ya ce ƙamus ɗin wani muhimmmin cigaba ne a fannin koyarwa da kuma bincike a harshen Hausa.

Kazalika Paul ya ce, “a cikin shekaru 50 daidai da na shafe a Kano sun taka muhimmiyar rawa wajen nasarar rubuta wannan littafi.

“Idan aka yi la’akari da yawan Hausawa a duniyar nan da masu amfani da harshen Hausa, babu shakka ta na ɗaya daga cikin harsuna mafi muhimmanci a Afirka, kuma ɗaya daga cikin manya a duniya,” inji Paul.

Tun farko a jawabinsa, Shugaban Jami’ar ta Bayero, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya ce ƙaddamar da littafin ’yar manuniya ce kan irin gudunmawar BUK a ɓangaren ilimi.

Mahalarta taron ƙaddamarwar

“BUK na ɗaya daga cikin ja-gaba a cikin jerin cibiyoyin ilimi wajen koyar da Hausa a ciki da wajen Nijeriya. Mawallafin wannan littafin sananne ne a fannin harsuna.

“Kuma sai da muka kafa kwamitin masana harsuna suka yi nazari sannan suka bada shawarwari, kuma marubutansa suka karɓa suka yi murna, kafin a kammala shi,” inji Farfesa Sagir.

Taron dai ya samu halartar manyan mutane da suka haɗa da: Jakadiyar qasar Poland a Nijeriya, Joanna Tarnawska da mataimakiyarta Khadija Alƙali, da Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da sarakunan Kazaure da Ƙaraye, da kuma wakilan gwamnonin jihohin Kano da Bauchi da Jigawa da Katsina da kuma wakilin babban mai ƙaddamarwa Dr. Alhaji Aminu Alasan Ɗantata.