Jamiar Carolina ta dau gwamna Ganduje aikin koyarwa

Cibiyar nazarin fasahar sadarwa da watsa labarai ta jami’ar Carolina dake kasar Amurka, ta amince da ta dauki gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin mai horaswa a cibiyar. Wannan sanarwa ta fito ne a yau din nan, ta bakin kakakin gwamnatin malam Auwal Anwar.

A wata takarda da kakakin ya fitar, ta bayyana cewa, an bashi wannan aiki ne, saboda irin amannar da shugaban jamiar Farfesa Victor Mbarika, yayi da salon mulkin gwamna Ganduje da kuma irin wanda ya sanyawa takardar daukan aikin rawar da gwamnatinsa ke takawa, wurin cigaban al’umma.

Wasikar dai wadda shugaban cibiyar ya sanyawa hannu, ran 30 ga watan Nuwamba, ta shaida cewa, an dauki gwamna Ganduje ne a matsayin jagora ga daliban da ke karatun digirinsu na uku da kuma kananan malaman jamiar.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*