Jamiar Dutse: Ana zargin gwamna Badaru da katsalandan

Wani rikici ya barke a jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutse jihar Jigawa, sakamakon zargin da ake na gwamnan jihar Alhaji Badaru Abubakar ya yi katsalandan a zaben.

A sakamakon haka wani gungun matasa ya mamaye makarantar, dalilin da ya hana cigaba da tantance masu neman zama mataimakin shugaban jami’ar. Matasan dai sun nuna cewa, lallai sai dai dan asalin jihar Jigawa ne zai zama mataimakin shugaban jami’ar.

A wani bincike da jaridar Manhaja ta yi, ta gano cewa, matasan na zargin an sanya wasu ka’idoji da za su iya zama tarnaki ga dan takarar zama mataimakin shugaban jami’ar, wanda dan asalin jihar ne ta Jigawa. A sakamakon haka, gwamnan ya nemi ganawa da yan kwamitin tantancewar, domin ganin yadda za a yi a sassauta ka’idojin saboda dantakarar ta sa ya samu haye wa. An dai ce a yayin wannan taro, gwamnan ya gargadi yan kwamitin da in suka kuskura su ka zabo wani wanda ba dan yankin Arewa maso yamma ba, ko kuma dan jihar Jigawa, to zai dau matakan da za a rushe hukumar zartarwar makarantar. Hakan kuma ana ganin zai zama tarnaki ga burin wani farfesa dan asalin jihar Borno.

Sai dai an ji gwabnan na cewa, ya shiga maganar ne, domin hana aukuwar fitina amma ba shi da wani dan takara da ya ke so. wani mai magana da yawun gwamnan ya ce “gwabna Badaru mutum ne mai son zaman lafiya, kuma ba zai yadda ya ajiye cancanta saboda akidar bangaranci ba, ya dai shiga maganar ne dan saboda hana aukuwar fitina da ka iya tasowa”.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*