Daga ABDULLAHI
MUHAMMAD a Katsina
Jami’ar Gwamnatin Tarayya FUDMA da ke Dutsinma a Jihar Katsina zata yi bikin yaye ɗalibai a karo na tara inda za ta karrama uwargidan shugaban ƙasa da wasu fitattun mutane su uku.
Mataimakin jami’ar Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi ya faɗi haka a hira da manema labarai da yayi a ɗakin taro na jami’ar.
Yace uwargidan shugaban ƙasan ta taka rawar gani wajen ilimin ɗalibai mata a jami’ar.
Farfesa Bichi ya bayyana cewa a lokacin da ƴan bindiga suka sace wasu ɗalibai mata na jami’ar, ta taka rawa gaya wajen kuɓutar da su .
“Bayan kuɓutar da ɗaliban sanata Reni Tinubu ta sa aka kai su wajen ta a Abuja ta basu gurbin ƙaro karatu tare da basu Naira miliyan biyu kowannen su.
Yace jami’ar za ta karrama sanata Remi Tinubu da digiri akan harkar siyasa.
Sauran waɗanda za a karrama sun haɗa da shugaban majalisar dattijai Sanata Godswill Akpabio da Sanata Aliyu Magatakarda da kuma shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar wakilai Hon Abubakar Aliyu Abubakar.
“Ɗalibai guda 4502 suka sami shaidar kammala karatun digiri a fanni daban daban a bana”yace.
Mutunlm 44 suka sami digiri aji na farko sai kuma guda 872 da suka sami digiri aji na biyu.
Asabar mai zuwa za ayi bikin yaye ɗaliban a filin wasa na jami’ar a Dutsinma.