Jami’ar Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Azare ta ɗauki ɗaliban farko guda 760

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Sabuwar Jami’ar Kimiyyar Ilimin Kiwon Lafiya ta Gwamnatin Tarayya da take da mazauni a garin Azare cikin Jihar Bauchi ta ƙaddamar da ɗalibanta na farko guda 760 na zagon karatu na shekarun 2021/2022 da 2022/2023.

Da yake yin matsakaicin jawabin fara karatun ɗaliban a garin Azare, muƙaddashin shugaban jami’ar, Farfesa Bala Mohammed Audu ya ce Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ne ya kafa jami’ar a watan Yuni na shekara ta 2021, kazalika an naɗa shugabanninta ne bada wani ɓata lokaci ba a ranar 27 ga watan Janairu na shekara ta 2022.

“Yau muna yin jawabin fara karatun ɗaliban farko bisa tsare-tsare guda biyar da suka jiɓanci tsangayoyin karatu guda bakwai waɗanda a turance sun haɗa da “Medicine, Dentistry, Nursing, Nutrition/Dietetics da Radiography”.

Mun rantsar da ɗalibai 550 na zangon karatun shekarar 2022/2023 da kuma ɗalibai guda 210 na zangon karatun shekarar 2021/2022 waɗanda a jimlace suka kama ɗalibai 760 ke nan.”

Farfesa Audu ya kuma bayyana cewar, Hukumar Gudanar da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) da Majalisar Kiwon Lafiya ta Nijeriya (MDCN) dukkansu sun rattaɓa umarnin ɗauka da horar da ɗaliban ilimi da ilimin kiwon lafiya na ɗaukar mafi ƙarancin ɗalibai masu karatun ilimin kiwon lafiya guda 100, “saboda haka yau muna zaunar da ɗalibai masu koyon ilimin kiwon lafiya guda saba’in na shekarar 2021/22 da guda cas’in ɗaliban MBBS na shekarar karatu ta 2022/2023.

“Kazalika, mun buɗe karatun ɗalibai majiɓanta koyon ilimin kula da lafiyar haƙori guda talatin na shekarar karatu ta 2021/22 da ɗalibai guda hamsin na koyon zallar ilimi na shekarar karatu na 2022/23 bisa amincewa da hukumar kula da jami’o’in ƙasar nan (NUC) da MDCN suka yi.

“Muna gabatar da ɗalibai guda saba’in masu koyon ilimin likitanci (BNS) na zangon karatu na shekarar 2021/22 da na shekarar 2022/23. Wannan shi ne mafi cancantar kwas ko manhajar karatu da ake. Mune na biyu daga cikin jami’o’i goma sha uku dake cikin shiyyar Arewa maso Gabas dake da wannan manhaja ta karatu.”

Audu ya bayyana cewar, jami’ar ta Azare ta kuma ɗauki wasu ɗalibai da za su yi karatu kan manhajjoji daban-daban, yana mai cewar akwai dalilin da ya sanya jami’ar ta ɗauki ɗalibai kaɗan, duk da cewar, ɗalibai fiye da dubu goma suka nuna shiga jama’ar tunda farko, yana alaƙanta lamarin da hukumar jarrabawa ta JAMB da kuma NUC waɗanda suka umarci jami’ar ta ɗauki ɗalibai guda ɗari biyar kacal.