Jami’ar Ladoke ta haramta wa ɗalibai zuwa makaranta da motocinsu

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Jami’ar Ladoke Akintola (LAUTECH) da ke Ogbomoso ta haramta wa ɗalibai tuƙa motoci a cikin jami’ar da kuma shiga harabarta da motocin kansu.

Rijistaran jami’ar, Dr. K.A. Ogunleye, ya ce hukumar jami’ar ta cimma wannan matsaya ne yayin taron da ta gudanar ranar Laraba, 22 ga Maris, 2023.

Sanarwar da Hukumar Jami’ar ta fitar ta ce, “Daga yanzu an haramta wa ɗalibai shiga jami’ar da motocin kansu.”

“Haka nan, ta haramta wa motocin da ba su da lambar rijista shiga jami’ar.

Sai kuma batun ajiye motoci ba a bisa ƙa’ida ba a harabar jami’ar wanda hukumar jami’ar ta ce ba za ta lamunci ci gaba da ganin ana aikata hakan ba.

Kazalika, hukumar ta haramta amfani da gilashin mota mai duhu ga malamai da ma ɗaliban.

Ta ce duk wanda aka kama da take wannan doka ko umarni, ɓangaren tsaron jami’ar zai yi aikinsa.