Jami’ar Legas na shirin tilasta wa ɗalibai ɗaukar darasin Yarabanci

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Jami’ar Jihar Legas (LASU) a wani yunƙuri na kare martabar al’adun gargajiyar Nijeriya, ta sanar da shigar da harshen Yarabanci a matsayin kwas na tilas ga ɗaukacin ɗalibanta.

Sabon kwas da aka ƙara a cikin manhajar makarantar daga zaman karatun 2023/2024 mai suna GNS 104 (Nazarin Harshen Yarabanci).

Shawarar da LASU ta yi na gabatar da wannan kwas ɗin ya yi daidai da ƙoƙarin da ake yi na ƙasa baki ɗaya na kiyaye al’adun gargajiya da al’adu daban-daban na Nijeriya.

Kwas ɗin, Nazarin Harshen Yarbanci, an tsara shi ne don baiwa ɗalibai cikakkiyar fahimtar harshen Yarbanci, ɗaya daga cikin fitattun harsunan ’yan asalin Nijeriya.

Yana da nufin ba ɗalibai ƙwarewar harshe, ilimin al’adu, da mahallin tarihi, haɓaka zurfin godiya ga al’adun Yarabawa.

Da ya ke nasa jawabin shugaban tsangayar fasaha da al’umma ta LASU Farfesa T.M Salisu ya bayyana farin cikin sa na qaddamar da kwas din. Ya jaddada yuwuwar sa don ƙarfafa haɗin gwiwar ɗalibai zuwa tushen su da haɓaka bambancin al’adu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *