Jami’ar NOUN ta yi sabbin naɗe-naɗe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Majalisar Gudanarwar Jami’ar NOUN ta Nijeriya, ta amince da naɗin sabon magatakarda, shugaban kula da shige da ficen kuɗaɗe da kuma shugaban ɗakin karatu, na wa’adi guda na shekaru biyar.

Sabbin waɗanda aka naɗa sune, Oladipo Adetayo Ajayi a matsayin magatakarda, Malam Nasir Gusau Marafa a matsayin shugaban kula da shige da ficen kuɗaɗe da Dakta Angela Ebele Okpala a matsayin shugaban ɗakin karatu na jami’ar.

An miƙa naɗin ga waɗanda aka naɗa a wasiƙu daban-daban na ranar 27 ga watan Yuni, 2022, kuma magatakarda mai barin gado, Felix I. Edoka ya sanya wa hannu.

Edoka ya ce, majalisar gudanarwar jami’ar ta amince da naɗin guda uku ne a taronta na 69 da ta gudanar a ranar Alhamis, 23 ga watan Yuni, 2022.
A cewarsa, sabon naɗin magatakardar zai fara aiki daga ranar 5 ga Satumba, 2022.

A gefe guda, sabon naɗin na shugaban kula da shige da ficen kuɗaɗe, a cewar magatakardar, zai fara aiki daga Satumba 17, 2022, yayin da naɗin shugaban ɗakin karatu na Jami’ar zai fara aiki daga Yuni 23, 2022.