Jami’ar UNIZIK ta kori ɗalibar da ta casa lakcara

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Nnamdi Azikwe, ta tabbatar da korar wata ɗaliba mai suna Goddy-Mbakwe Chimamaka Prescious, bayan samun ta da laifin lakaɗa wa malami duka akan bidiyon TikTok a jami’ar.

Rajistiran riƙon ƙwarya na jami’ar, Victor Modebelu ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Juma’a.

Ya ce Shugaban jami’ar ya samu rahoto daga kwamitin hukunta ɗalibai akan dukan da ta yi wa wani lakcara daga tsangayar nazarin wasan kwaikwayo.

Sanarwar ta ce an kama Chimamaka ne da laifin rashin ladabi da ƙarya dokokin kundin dokar zama ɗalibi, wanda a saboda haka ne aka zartar mata da hukuncin kora daga jami’ar.