Daga BELLO A. BABAJI
Wani jami’in ƴan sanda ya samu rauni a yayin wani harin da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka kai a wani ofishin rundunar dake Jihar Borno.
Lamarin ya auku ne a Jakana, a safiyar ranar 28 ga watan Nuwamba.
Kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi ya tabbatar da faruwar al’amarin cikin wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi, inda ya ce ƴan sandan ne suka mayar da martani ga harin mayaƙan wanda a yayin haka ne jami’i ɗaya ya samu raunin harbin bindiga da hakan ya sa aka garzaya da shi asibiti don karɓar kulawa.
Haka kuma a yayin martanin ne jami’an suka raunata da dama daga cikin mayaƙan tare da kora su.
A wani labarin kuwa, jami’an tare da haɗin-gwiwar wasu hukumomin tsaro sun gudanar da atisaye a Sakkwato, a sansanin ƴan ta’adda.
A nan ne suka yi nasarar tarwatsa su tare da ƙwato muggan makamai da suka haɗa da bindigu ƙirar AK47 da tarin alburusai.
Haka ma a Jihar Delta, ƴan sandan sun yi arangama da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne inda aka yi ta ba-takashi a tsakanin su wanda hakan ya bai wa jami’an damar kora su bayan raunuka da suka samu na alburusai.