Jami’in tattara sakamakon zaɓen Sanatan Kebbi ta Tsakiya ya yi ɓatan-dabo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta dakatar da harhaɗa sakamakon zaɓen Sanatan Kebbi ta Tsakiya sakamakon ɓacewar jami’in da ke wakiltar mazaɓar Marafa, a Birnin Kebbi.

An buƙaci ya koma gefe ya daidaita wasu bambance-bambance a cikin alƙaluman sakamakon da ya kawo wa cibiyar tattara bayanan lokacin da ya ɓace kuma ba a iya gano shi ba tun ranar Lahadi.

Jami’in tattara sakamakon zaɓen, ya yi ɓatan-dabo ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Lahadin da ta gabata.

Sakamakon da ake magana a kai na tsakanin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu da Sanata Muhammad Adamu Aliero.

Ya zuwa yanzu dai an tattara sakamakon ƙananan hukumomi bakwai daga cikin ƙananan hukumomi takwas da suka ƙunshi mazaɓar Kebbi ta Tsakiya.

Wakilan jam’iyyun siyasa a cibiyar tattara sakamakon zaɓen sun nuna damuwarsu kan matsalar da aka samu musamman yadda INEC ta kasa yanke shawarar abin da za ta yi game da lamarin.

Wani jigo a Jam’iyyar PDP, Alhaji Sani Dododo ya shaida wa manema labarai a cibiyar tattara sakamakon cewa ba za su tayar da hankalin jama’a ba game da wannan matsalar, amma idan INEC ta ƙi yin wani abu cikin ‘yan mintoci masu zuwa game da ɓacewar jami’in za su bayyana wa duniya.

“Muna jira su yi wani abu a kai. Idan muka ɗan dakata ba tare da komai daga INEC da jami’an tsaro a nan za mu gaya wa duniya abin da ke faruwa a yanzu,” inji shi.

Da aka tuntuɓi kwamishinan zaɓe na garin, Barista Ahmed Bello Mahmud ya ce zai samu labarin yadda ake ciki daga jami’in zaɓen na Birnin Kebbi domin sanin matakin da za a ɗauka na gaba.