Jam’iyyar AAC ta fatattaki Sowore a ofishin INEC

Daga FATUHU MUSTAPHA

‘Ya’yan jam’iyyar African Alliance Congress (AAC) sun ce suna kan bakansu na korar da suka ce an yi wa Omoyele Sowore daga jam’iyyarsu har ma da neman ‘yan sanda su kama shi saboda shigan burtun da suka ce ya yi musu.

A wannan Litinin ne wani gungun mutane ƙarkashin jagorancin Sowore suka yi yinƙuri mamaye hedikwatar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a Abuja amma sai ‘yan jam’yyar AAC ƙarƙashin jagorancin shugabansu na ƙasa, Dr. Leonard Nzenwa, suka fatattake su.

Binciken Manhaja ya gano cewa, Sowore da mutanensa sun ziyarci ofishin INEC ne da nufin hargitsa wa hukumar lamurra amma kuma sai haƙarsu ta kasa cim ma ruwa.

Ɓabgaren Sowore na ƙoƙarin murza gashin baki ne domin ya zamana shi INEC ta sani a matsayin ƙirjin jam’iyyar AAC amma sai aka yi rashin sa’a ɓangaren Nzenwa ya riga ya shige gaba a matsayin wanda INEC ta sani game da jam’iyyarsu ta AAC.

‘Yan jam’iyyar sun ce ba su hana Sowore yin zanga-zanga ba, amma cewa ba su yarda ya yi amfanin da jam’iyya ba wajen neman cim ma buƙatarsa saboda shi korarre ne a jam’iyyar.

A cewar Nzenwa said, “Ranar Laraba ta makon jiya, mun kwarmata wa ƙasa wata maƙarƙashiya da ake shirya wanda ake so a fake da jam’iyyarmu wajen don tada hargitsi da kuma ƙona ofisoshin INEC a faɗin ƙasa, tare da aniyar kai hare-hare kan kadarorin al’umma don tada rikici a ƙasa.”

AAC ta ce, da farko sai da ta ɗauki matakin dakatar da Sowore kafin daga bisani ta kore shi daga jam’iyyar baki ɗaya saboda rashin tafiya daidai da dokokin jam’iyya.