Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta yaba da yadda sojoji suke murƙushe ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jam’iyyar APC reshen Kihar Zamfara ta yabawa sojojin Nijeriya tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro bisa nasarorin da ake samu na kawar da ‘yan bindiga a yankin Arewa maso yamma.

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na jihar, Yusuf Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Gusau a ranar Litinin.

Jam’iyyar ta yabawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin bai wa sojoji damar gudanar da aikin ba tare da wata matsala ba, wanda ƙaramin ministan tsaro, Dakta Bello Mohammed Matawalle ke jagoranta.

“Muna tare da sauran ‘yan ƙasa nagari wajen murnar waɗannan muhimman nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu wadda take kawar da wasu manyan ‘yan bindiga da suka haɗa da ɗan Bello Turji da ƙanen Adamu Alero.

“Ayyukan da sojoji suka ƙaddamar a shekarar da ta gabata na Operation Fansan Yamma, wanda ƙaramin ministan tsaro, Bello Mohammed Matawalle, da babban hafsan hafsan tsaron kasa, Janar Christopher Gwabi Musa, suka ƙaddamar a Sokoto, na samun sakamako mai kyau, inda aka kawar da shugaban ‘yan bindiga, Halilu Sububu, da tawagar shi”.

Jam’iyyar ta bayyana yadda aka share maɓoyar Bello Turji a baya-bayan nan inda aka kashe ɗansa da wasu makusantansa a matsayin abin ban sha’awa, inda ta jaddada cewa hakan ya ƙara ƙwarin gwiwa ga sojoji a tsakanin ‘yan ƙasar.

Jam’iyyar ta yi nuni da cewa sanarwar da shugaban ƙasar ya yi na daƙile masu aikata laifuka da kuma kawo ƙarshen ayyukan su a shekarar 2025 da cewar abun farin ciki ne.

Jam’iyyar ta buƙaci ‘yan ƙasa masu son zaman lafiya da su ci gaba da bayar da goyon baya tare da baiwa sojoji bayanai masu inganci domin a samu sauƙin gano duk wasu miyagun ƙungiyoyin da suka haɗa da masu ɗaukar nauyinsu da masu ba da labari domin ganin an dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma.