Jam’iyyar PDP ta lallasa APC a gidan gwamnatin Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Jam’iyyar APC mai mulkin Jihar Kaduna ta sha kaye a akwatunan zaɓe biyun da ke Gidan Sir Kashim Ibrahim, fadar gwamnatin jihar.

Ɗan takarar gwamna na PDP, Alhaji Isa Ashiru Kudan ne ya lashe akwati mai lamba 014 da ƙuri’u 77 yayin da ɗan takarar APC, Sanata Uba Sani ya samu ƙuri’u 40.

Jami’in zaɓe Mohammed Baso ya ce jam’iyyun PRP da NNPP sun samu ƙuri’u ɗai-ɗaya.

Haka ma akwatu mai lamba 013 PDP ta yi nasara da ƙuri’u 69 yayinda APC ta samu 64.

Jami’in zaɓe Kalu Kelechi Michael ya ce jam’iyyar LP ta samu takwas, yayinda PRP da NNPP suka samu ɗai-ɗaya.