Jam’iyyarmu tana buƙatar taimakon kowa – Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullah Adamu ya buƙaci masu son tsayawa takara da su nuna halin haƙuri da kuma karɓar sakamakon taron hannu biyu-biyu.

Hakan na ƙunshe ne a jawabin karɓarsa bayan ya lashe zaɓen shugabancin jam’iyyar APC mai mulki a ranar Asabar a Abuja.

Sanata Adamu wanda ya taya maza da mata na jam’iyyar APC murna, ya kuma ja hankalin ’yan takarar da ba su yi nasara a wannan karon ba, ya ƙara da cewa nan da lokacin da Allah ya ƙayyade za su aiwatar da burinsu.

Ya ce, “a madadin takwarorina, zaɓaɓɓun mambobin kwamitin ayyuka na ƙasa na babbar jam’iyyarmu ta APC, ina miƙa godiyarmu ga Allah Maɗaukakin Sarki, godiya ta tabbata ga shugabanmu, Shugaban Tarayyar Nijeriya, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Gwamnonin Jam’iyyarmu, Shugaban Mambobin Kwamitin Tsare-tsare (CECPC), wakilan taron, ga dukkan shugabanninmu a matakai daban-daban, da ma ɗaukacin ’ya’yan babbar jam’iyyarmu ta ƙasa baki ɗaya da suka zaɓe mu a waɗannan muqamai masu matuƙar nauyi.

Sanata Adamu ya koka da cewa shekaru 7 da suka gabata jam’iyyar ta yi ta fafutukar inganta rayuwar ‘yan Nijeriya ta hanyar manufofi, shirye-shirye da ayyuka daban-daban.

Don haka ya yi kira da a sabunta tare da sake ɗaukar nauyin duk wani mai kishin jam’iyyar don magance rigingimun da suka dabaibaye jam’iyyar a dukkan matakai.

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ya yi alƙawarin samar da sulhu mai ɗorewa a tsakanin ’ya’yan jam’iyyar, inda ya ƙara da cewa, za su gudanar da manufar buɗe ƙofa ga ’ya’yan jam’iyyar.

Ya kuma bayyana cewa, a tarihin Nijeriya gwamnati ta taka rawar gani wajen gina muhimman ababen more rayuwa da kuma inganta rayuwar al’ummar Nijeriya.

Sanata Adamu ya roƙi ’yan jarida da kafafen yaɗa labarai da su farfaɗo tare da tabbatar da kishin ƙasa na waɗanda suka kafa sana’arsu.

Daga nan sai ya buƙaci kowa da kowa da su cigaba da kishin ƙasa tare da cigaba da yin aiki tuƙuru domin samun nasarar ƙasa.

Ya gode wa shugaba Buhari da sauran masu ruwa da tsaki bisa amincewar da aka basu, ya kuma yi alƙawarin cewa ba za su ɓata jam’iyyar da ’yan Nijeriya da Afrika gaba ɗaya su ka aminta da ita ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *