Jam’iyyun siyasa a Nijar sun taya murnar buɗe babban taron wakilan JKS karo na 20

Daga CMG HAUSA

A yayin da babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin karo na 20 ke gudana, jam’iyyun siyasar Nijar sun aike da wasiƙu, zuwa ga kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin, da babban sakataren kwamitin ƙolin jam’iyyar Xi Jinping, domin taya murnar nasarar da aka cimma ta gudanar da babban taron.

Shugaban riko na jam’iyyar PNDS-Tarayya mai mulkin Nijar, kuma babban wakilin shugaban ƙasar, Foumakouye Gado ya bayyana cewa, a ƙarƙashin jagorancin babban sakatare Xi Jinping, ƙasar Sin ta samu gaggaruman nasarori a fannonin zamanantar da al’ummar ƙasar, kana ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya.

Ya ce, jam’iyyarsa tana taya murnar shirya babban taron wakilan JKS karo na 20 cikin nasara, kuma ta yi imanin cewa, taron zai ƙara inganta hadin kan al’ummar ƙasar Sin.

Kaza lika PNDS-Tarayya na fatan ƙarfafa haɗin gwiwa da jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin, don ƙara kyautata ‘yan uwantaka.

Shi kuwa a cikin ta sa wasiƙar taya murnar, shugaban jam’iyyar MNSD-Nassara, kuma shugaban majalisar dokokin ƙasar Seini Oumarou, ya taya jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin murnar jagorantar jarumtar jama’ar ƙasar Sin, wajen samun gagarumar nasarar ‘yantar da ƙasa, da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.

Mai fassara: Bilkisu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *