Daga BELLO A. BABAJI
Ƙasar Jamus dake Nahiyar Turai ta yi kira ga Isara’ila da ta bari a kai ƙarin kayan agaji na jinƙai zuwa Arewacin Gaza a ƙasar Palestine.
Kakakin Ma’aikatar waje ta Jamus ya bayyana hakan a inda ya ce, “Mu na kiran gaggawa ga Gwamnatin Isra’ila ta yi abin da yake wajibi ne a kanta ƙarƙashin dokar ƙasa-da-ƙasa.”
Jakadan Palestine a Nijeriya, Abdallah Abu Shawesh ya ce watanni 13 kenan da ake cigaba da buɗe wuta da tarwatsa garuruwa da hana a kai kayan tallafi ga Falasɗinawa.
Ya ce, su na kira ga Jamus da ta daina kai wa Isra’ila makamai ta yadda ita ma Jamus za ta zama ta kiyaye dokar ƙasa-da-ƙasa da na Majalisar Ɗinkin Duniya.
Jakadan ya kuma ce, “Mu na kira ga Jamus da ta taimaki aikin Kotun Laifukan Ta’addanci ta ƙasa-da-ƙasa wajen tabbatar hukunta waɗanda ke da hannu a laifukan yaƙi.”
Haka nan, Abu Shawesh ya yi kira ga Ministan Harkokin Waje na Jamus da ya ƙaurace wa amincewa da ikirarin Isra’ila na tabbatar da kashe Falasɗinawa saboda su na yankunan da hare-hare suka fi ƙarfi, wanda hakan hana musu ƴancin ba su kariya ne.