Jan aikin da ke gaban Erik ten Hag a Man United

Ranar Litinin sabon kocin Manchester United, Erik ten Hag ya fara jan ragamar atisayen ƙungiyar, domin shirin tunkarar kakar bana.

Ranar 21 ga watan Afirilu aka sanar da ɗaura Tem Hag a matakin kocin United daga Ajax, domin maye gurbin Ralf Rangnick.

United wadda ta yi ta shida a gasar Premier League da aka ƙarƙare, za ta fara buga babbar gasar ƙwallon ƙafa ta bana ranar 7 ga watan Agusta, inda za ta karɓi baƙuncin Brighton.

’Yan ƙwallo tara Ten Hag ya samu yin atisaye tare da su daga cikin waɗanda ke buga wa United wasanni da suka haɗa da De Gea da Heaton da Phil Jones da Lindelof da Martial da kuma Rashford.

Sauran sun haɗa da Sancho da Tuanzebe da Van de Beek da wasu matasa da suka haɗa da Alvaro Fernandez da Alejandro Garnacho da Zidane Iqbal da Charlie Savage da Shola Shoretire da kuma Charlie Wellens.

Manchester United ce kan gaba a yawan lashe Premier League, mai 20 jumulla.

A lokacin da Sir Alex Ferguson ke jan ragamar ƙungiyar ta taka rawar gani a Ingila da Turai da faɗin duniya, amma a yanzu zancen ya sauya.

Rabon da United ta ɗauki Premier League tun bayan 2013, idan kuma kofin zakarun Turai ne tun bayan wanda Jose Mourinho ya ɗauki Europa League a 2016/17 – yanzu shekara biyar kenan.