Janar Attahiru: An kammala rahoton binciken hatsarin jirgin da ya yi ajalinsa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kwamishina kuma Babban Jami’i a Hukumar Binciken Hatsarin Jiragen Sama (AIB), Engr. Akin Olateru ya miƙa rahoton hatsarin jirgin sojin da ya yi ajalin Tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa, na Laftanar Janar Ibrahim Attahiru wanda ya afku yayin da zai sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na ƙasa da ke Kaduna.

A ranar Laraba kwamitin biciken ya miqa rahonsa ga Babban Hasfan Sojin Sama, Air Marshal Oladayo Amao, wanda shi ne ya kafa kwamitin na ‘AIB’ da haɗin gwiwar rundunar domin gano musabbabin hatsarin.

Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ya rasu ne tare da ‘yan tawagarsa mutum 12 a hanyarsu ta halartar bikin yaye kuratan sojoji a Zaria, bayan jirgin samfurin Beechcraft King Air 350, ya yi hatsari ya ƙone ƙurmus, babu wanda ya tsira a cikinsu a ranar 21 ga Mayu, 2021.

A jawabinsu, Kakakin Rundunar, Air Commodore Edward Gabkwet, da takwaransa na AIB, Tunji Oketunbi, sun ce rahoton ya ƙunshi bayanan da aka tattara a yayin binciken, sharhinsu da kuma abubuwan da aka gano da ma shawarwari.

Sanarwar da suka fitar ta ce, “A lura cewa a matakin farko, an gano abubuwa 27 tare da bayar da shawarwari takwas na tsaron lafiya waɗanda rundunar da sauran mahukunta za su aiwatar.

“Rahoton zai bayyana abin da ke ƙunshe cikin na’uarar naɗar bayanan jirgin, da tsarin masu kula da shi da kuma sharhin kowannensu.”

Da yake karɓar rahoton, shugaban rundunar, ya ce manufar binciken ita ce tabbatar da aminci a sufurin jiragen sama, ba wai kawai a gano mai laifi da kuma hukunta shi ba.

A cewar sa, haɗin gwiwar alama ce ta ƙarfi da ingancin da ake buƙata a harkar binciken hatsarin jiragen sama da kuma yin komai a fili, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A nasa ɓangaren, Shuagaban AIB, Injiniya Akin Olateru, ya ce binciken haɗin gwiwar shi ne irinsa na farko da AIB ta yi tare da rundunar, kuma na biyu da ta yi tare da wata hukumar soji.

Ya bayyana cewa za a miƙa kwafin rahoton ga Ministan Sufurin Jiragen Sama da Hukumar Kula da Sufurin Jirage Sama (NCAA) domin ganin an aiwatar da shawarwarin da ke ƙunshe a ciki.

Ya ce duk da cewa jirgin soji ne, hatsarin ya auku ne a filin jirgin farar hula, kuma haɗin gwiwar ta taimaka wajen rufe giɓin da ke akwai a ɓangaren sufurin jiragen sama.