Janar Yahaya ya buƙaci kyautata hulɗa tsakanin sojoji da fararen hula

Babban Hafsan Rundunar Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya yi kira da a samar da faɗaɗɗen tsari na hulɗa tsakanin soji da fararen hula domin inganta kundin tsarin hulɗa tsakanin sojoji da fararen hula da masu ruwa da tsaki a Najeriya.

Yahaya ya yi wannan kira ne yayin gabatar da lacca ga mahalarta darasi na 43 na cibiyar koyar da dabaru da siyasa na tarayya da ke Kuru, Jos babban birnin jihar Filato.

Jami’in ya bayyana cewa, rundunonin sojin ƙasa na aikin ƙirƙiro dangantaka mai ƙarfi domin ƙara kyautata hulɗa domin samun nasara wajen yaƙi da ta’addanci.

Daga nan, ya buƙaci a inganta samar da muhimman bayanai tsakanin soji da fararen hula don kyautata hulɗa tsakanin ɓangarorin biyu.

Kazalika, ya buƙaci ƙirƙiro kundin hulɗa da jama’a da dabaru, tare da neman a samar da tsarin haɗin gwiwa tsakanin soji da fararen hula da kuma samar da kasafin kuɗi domin aiwatar da tsarin.

Sanarwar da ta fito ta hannun Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, mai ɗauke da kwanan wata 29 ga Satumba, ta nuna cewa yayin taron Yahaya ya gana da mahalarta tare da jami’an cibiyar a yayin ziyarar aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *